Peter Obi Ya Yi Martani Kan Dakatar da Betta Edu, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Tinubu

Peter Obi Ya Yi Martani Kan Dakatar da Betta Edu, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Tinubu

  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya bukaci gudanar da cikakken bincike kan badakalar naira miliyan 585 a ma'aikatar jin kai
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bukaci gwamnatin tarayya da Shugaban kasa Tinubu ke jagoranta da ta hukunta abokan harkallar Betta Edu
  • Don haka Obi ya ayyana goyon bayansa a yaki da ake da cin hanci da rashawa, yana mai dagewa kan lallai a bi diddigi a gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan takararjam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, kan dakatar da ministar jin kai, Betta Edu kan badakalar naira miliyan 585.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Peter Obi ya yaba ma Tinubu kan dakatar da Betta Edu
Peter Obi Ya Yi Martani Kan Dakatar da Betta Edu, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dr Betta Edu
Asali: Facebook

Obi ya fadi matakin dauka kan masu hannu a badakalar

A wasu jerin rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa dakatar da Betta Edu bai wadatar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maimakon haka, Obi ya nemi a gudanar da gagarumin bincike a kan badakalar kudin.

Obi ya kuma nuna sha'awa a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, inda ya bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya tabbatar da ganin cewa "an yi cikakken bincike domin a gurfanar da duk masu laifi a gaban kuliya."

Obi ya rubuta:

"Batun Betta Edu da lamura masu alaka
"Ina so in kara da muryata da na mafi akasarin yan Najeriya da suka damu da bin diddigi a gwamnati da kuma yin amfani da kudaden jama'a yadda ya dace, ina maraba da dakatar da ministar jin kai, Misis Betta Edu, da kuma umarnin bincikenta.

Kara karanta wannan

“Sai wata rana PDP”: Na hannun damar Atiku ya gana da Tinubu a Villa, hoto da bidiyo sun bayyana

"Yayinda gwamnati ta dauki matakin da ya dace, dole ne binciken ya zama cikakke domin a gurfanar da duk wadanda ake zargi a gaban doka."

Obi ya ce kada a tsaya a iya dakatar da ministar, maimakon haka a tsamo duk wadanda ke da hannu a badakalar sannan a hukunta su kamar ministar.

Ndume ya magantu kan badakalar Betta Edu

A wani lamari makamancin wanna, mun ji cewa bulaliyar majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan gaggauta dakatar da ministar jin kai da yakar talauci, Dr Betta Edu, da ya yi a kan badakalar naira miliyan 585.

Sanatan ya bukaci shugaba Tinubu da ya duba wuce gona da iri na wadanda ya bayyana a matsayin ‘barayin 'yan siyasa masu tasowa', kuma ya yi gargadin cewa hakan na iya zama mafi muni fiye da wadanda ake kira da 'cabal' idan ba a dauki mataki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel