N2.5tr: Kamfanin NNPC Ya Samu Ribar Da Ba a Taba Ji ba a Shekaru 47 a Zamanin Tinubu

N2.5tr: Kamfanin NNPC Ya Samu Ribar Da Ba a Taba Ji ba a Shekaru 47 a Zamanin Tinubu

  • A shekarar da ta wuce watau 2022, kamfanin NNPC Ltd ya samu ribar fiye da Naira Tiriliyan 2.5
  • Kafin zuwan dokar PIA, an yi shekara da shekaru, babu abin da NNPCL yake samu sai asara
  • Bayanan da aka fitar a makon nan ya tabbatar da kamfanin man Najeriyan ya kafa tarihi a bara

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kamfanin man Najeriya watau NNPC Ltd., ya sanar da cewa ya samu ribar N2.548tn a cikin shekarar 2022.

A ranar Talata, kamfanin NNPC Ltd ya bada sanarwar samun ribar da ta fi kowace tun da aka kafa ta a shekarar 1977.

NNPCL
Shugaban kamfanin NNPCL Hoto: Mele Kyari Credit: Bloomberg/Getty Images
Asali: Getty Images

An fara samun riba a kamfanin NNPCL

Punch ta ce kamfanin ya canza salo a Agustan 2021 bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a dokar PIA.

Kara karanta wannan

Dalibi ya gwangwaje tsohon malaminsa da kyautar sabuwar mota da kudin mai na wata 12

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin gwamnatin Najeriyan ya koma kasuwanci da gaske musamman bayan tabbatar da cire tallafin man fetur a 2023.

Asara da ribar NNPCL a cikin shekaru 5

Bayanin da aka samu daga NNPCL ya nuna kamfanin man ya yi asarar N803bn a 2018.

Zuwa shekara mai zuwa ta 2019, sai asarar ta ragu zuwa 2019. A 2020 kuwa an samu ribar N287bn wanda ta canza lamarin.

A karkashin jagorancin Mele Kolo Kyari, a 2021, kamfanin man ya ci ribar N674.1bn wanda ya faru zuwa N2.458tr a 2022.

The Cable ta ce kamfanin zai fito da cikakken rahoton kudin da aka kashe da wanda aka samu a shekarar 2022 da ta gabata.

NNPCL na kama masu satar danyen mai

A sanarwar da aka fitar, kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ya gano matatun tace mai na karya 52 a Neja Delta a mako guda.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Za a kori dinbin mutane daga wuraren aiki a dalilin karyewar Naira

A kokarin maganin masu satar arzikin Najeriya, kamfanin NNPCL ya bankado yadda ake fasa kaurin danyen mai a Akwa Ibom.

Rahoton ya ce NNPC ya gano miyagu na sace danyen mai a garuruwan Warri da Bayelsa, an kuma yi nasarar kama mutane 17.

Za a kara farashin fetur?

Kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPCL yace ba a biyan tallafi kamar yadda bankin duniya da 'yan kasuwa su ke zargi.

Har yanzu ana sayen man fetur ne a kan N617-N690, duk da ikirarin cire tallafi tun 2023, wasu sun ce ya kamata farashin lita yt canza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel