Dalibi Ya Gwangwaje Tsohon Malaminsa da Kyautar Sabuwar Mota da Kudin Mai Na Wata 12

Dalibi Ya Gwangwaje Tsohon Malaminsa da Kyautar Sabuwar Mota da Kudin Mai Na Wata 12

  • A wani abin nuna godiya ta samun ilimi, wani dalibi ya ba tsohon malamin sa kyautar sabuwar a jihar Anambra
  • Bai bar malamin haka nan ba, sai da ya ba shi naira dubu 100 don shan mai, da naira dubu 30 don yin gyare-gyare a idan akwai
  • Malamin ya nuna tsantsar jin dadinsa, musamman yanzu da ya cika shekara 50 a duniya, bayan shafe shekaru 40 yana koyarwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Anambra - Wani Dr. Dominic Nwankwo, ya ba tsohon malamin sa a makarantar St. John Bosco Seminary da ke Isuanicha a jihar Anambra kyautar sabuwar mota.

Da ya samu rakiyar wasu daga cikin abokan karatunsa a lokacin, Dr. Nwankwo ya kuma ba malamin kyautar naira dubu 100 don shan mai na tsawon shekara daya.

Kara karanta wannan

Mutane 5 wadanda suka fi karfin fada-aji a gwamnatin Buhari da yanzu aka daina jin duriyarsu

Dalibi ya ba malami kyautar mota
Dalibi ya gwangwaje tsohon malaminsa da kyautar sabuwar mota da kudin mai na wata 12. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Dr. Nwankwo ya fadi dalilin yi wa tsohon malamin nasa kyautar mota

Bai barshi hakan nan ba, sai da ya ba shi naira dubu 50 domin malamin ya yi gyaran motar, tare da biyan kudin inshora na shekara uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke mika wadannan kyaututtukan a majami'ar St. Theresa Catholic, Nibo da ke jihar, Dr. Nwankwo ya godewa Msgr. Mgbamfulu kan koyar da su da ya yi, Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

"Mun samu kyakkyawar tarbiyya da ilimi daga malamin, kuma wannan tallafin karrama wa ce ta nuna godiyar mu musamman da ya ke cika shekara 50 a duniya."

Yadda malamin ya ji bayan samun kyautar mota da kudi

Msgr Mgbamfulu, ya shafe kusan shekarun aikinsa yana koyar da darasin Chemistry a makarantar kusan shekaru 40, rahoton New Telegraph.

Kara karanta wannan

Kwararru sun bayyana dalilai 5 da suka sa yara ke shan wahala a darasin lissafi a makaranta

Da ya ke jawabi yayin gabatar da kyaututtukan, Kwamred Celestine Oguegbu, wanda malami ne a jami'a, ya ce tallafin zai nuna darajar malamai a wajen daliban su.

Msgr. Mgbamfulu ya nuna matukar jin dadinsa da samun wannan kyauta, ya yi wa tsohon dalibin nasa fatan alkairi a rayuwarsa.

Kotu ta dauki mataki kan matashin da ya kashe limami a jihar Kano

A wani labarin, wata kotun Majistire da ke Kano, ta garkame matashin da ya kashe limami a Kano saboda ya hana su shan wiwi a kusa da masallaci.

An ruwaito cewa, kotun ta haɗa da mahaifin yaron ta kulle saboda ya boye ɗan sa bayan da yaron ya aikata danyen aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel