Tattalin Arziki: Za a Kori Dinbin Mutane Daga Wuraren Aiki a Dalilin Karyewar Naira

Tattalin Arziki: Za a Kori Dinbin Mutane Daga Wuraren Aiki a Dalilin Karyewar Naira

  • Darajar Naira ta na ta faduwa war-was musamman tun da aka daidaita farashin kudin kasashen waje
  • Kamfanonin kasar sun samu babban kalubale wajen neman dalolin da za su shigo da kaya daga ketare
  • Kungiyoyin ‘yan kasuwa sun nusar da gwamnatin tarayya tashin Dala zai taimaka wajen tashin talauci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Naira ta rasa kimanin 38.9% na darajarta a kan Dalar Amurka a kafar I & E da bankin CBN yake saidawa ‘yan kasuwa kudin waje.

Daga N745.19/$ a Oktoban 2023, farashin kudin Amurkan ya kai N1035.12/$ a farkon Junairun 2023 kamar yadda Punch ta fitar da rahoto.

Kasuwa
Tashin Dala zai haifar da talauci Hoto: Medium
Asali: UGC

Dala $1 ta zarce N1, 000

Hatta a babban banki na kasa, Naira ta karye a sakamakon daidaita kudin kasashen waje. ‘Yan canji su na saida Dala ne kan kusan N1, 220.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan kasuwa da masu kamfanoni sun koka a ranar Lahadi da cewa karyewar Nairar tana da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

Talauci zai karu a Najeriya inji LCCI, MAN

Kungiyar MAN da kungiyar ‘yan kasuwan Legas da wata kungiya ta masu kananan kamfanoni a Najeriya sun ce hakan zai jawo talauci.

Mutane za su rasa ayyukansu a kamfanoni a dalilin tashin da Dala ta ke yi a Najeriya. Nairaland ta tabbatar da labarin ranar Litinin.

Karuwar masu zaman banza a garuruwa

Idan abubuwa ba su yi sauki ba, MAN da LCCI sun ce kamfanoni da yawa za su daina aiki, hakan zai yi sanadiyyar karuwar zaman banza.

Babban manajan kamfanin Royal Foam Products Limited, Ezekiel Akhiromen ya ce daga waje su ke sayo 80% na sinadaran da ake aiki da su.

Kara karanta wannan

Dangote ya farfado, ya ci ribar da ba a yi tsammani ba a cikin kasa da mako 1 na 2024

Kamfanoni na barin Najeriya

Shugaban LCCI, Gabriel Idahosa ya yi makamancin wannan kuka, yake cewa kamfanoni za su yi ta barin Najeriya idan Dala ta ki sauka.

Idahosa ya ce yanzu akwai wadanda su ka bar kasuwanci a Najeriya, su ka koma Ghana bayan hasashen karin wahala da tsadar rayuwa.

Mataimakin shugaban NASSI na kasa, Segun Kuti-George, ya yi magana karshen makon jiya, ya haska bakar wahalar da kamfanoni ke sha.

Mista Kuti-George yake cewa dole masu kamfanoni su ke rage adadin ma’aikatansu domin ba za sui ya daukar nauyinsu a halin yanzu ba.

Tsadar man fetur a duniya

Rahoto ya nuna kasashe 21 kacal su ka fi Najeriya arahar farashin fetur a yau duk da a kan kusan N700 ake saida lita a gidajen mau.

Babu inda fetur yake tsada a yau kamar a biranen Monaco da Hong Kong inda lita ta kai kusan N3, 000 yayin da lita ta ke N26 a Iran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel