'Ba a Shawarce ni Kafin a Haifo ni ba', 'Yar Tiktok ta Maka Iyayenta a Kotu

'Ba a Shawarce ni Kafin a Haifo ni ba', 'Yar Tiktok ta Maka Iyayenta a Kotu

  • Wata shararriyar ‘yar tiktok, Kass Theaz ta maka iyayenta gaban kotu saboda haihuwarta tare da neman izinin ko tana da sha’awar zama ‘yarsu ba
  • Tuni labarin ya fara daukar hankalin jama’a, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta inda ake ganin rashin dacewar matakin da ta dauka
  • Amma a bayaninta 'yar tiktok din ta sanar da cewa ita ma tana da yara, kuma iyayen da ta yi kara kotu na neman hanyoyin kwace su daga kulawarta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA-Wata shahararriyar ‘yar tiktok, Kiss Theaz ta maka iyayenta gaban kotu saboda haihuwarta ta tare da neman izininta ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi alkawarin kawo karshen matsalar fetur kwanan nan

Tuni labarin ya fara daukar hankalin jama’a, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta inda ake ganin rashin dacewar matakin da ta dauka.

Kass Theaz
Kass Theaz, ba'amurikiyar 'yar tiktok ta maka iyayenta kotu kan haihuwarta ta tare da izininta ba Hoto: Kass Theaz (@isatandstared)
Asali: UGC

Amma a bayanin da ta wallafa a shafinta na tiktok Kiss Theaz ta sanar da cewa iyayenta sun yanke hukuncin haihuwarta amma ba su shawarce ta su ji ko tana son zama ‘yarsu ba, kamar yadda DW ta wallafa a shafinta na facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kass Theaz ta haifi yara?

Bayan ta bayyana cewa ta maka iyayenta gaban kotu saboda sun haife ta kai tsaye ba tare da neman izini ba, shararriyar ‘yar Amurka nan, Kass Theaz ta bayyana cewa ita ma tana da yara.

Wannan ikirari ya janyo cece-kuce ganin yadda ta nuna kyamar yadda nata iyayen suka haife ta ba tare da neman izininta ba.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Amma bayanin da ta yi ta cikin bidiyon da aka wallafa a shafinta na Kass Theas, ta ce yanzu haka iyayenta na neman kotu ta kwace yaran daga hannunta, lamarin da ta ce zai zo da babbar matsala ganin yadda ba ta da aikin yi.

Ta ce tana samun kudi da yaran saboda mahiafinsu yana biyanta kudin raino tun da ba su tare.

Kotu ta dauki mataki kan Murja Kunya

Mun kawo muku labarin yadda wata babbar kotu dake zamanta a jihar Kano ta dauki matakin bayar da belin Murja Kunya kan kudi N500,000.

Kotu da bayyana cewa za a bayar da belin ne idan Murja ta cika sauran sharuddan da suka hada da kawo mutune biyu su tsaya mata, kuma dole sai da wani na kusa da ita cikin utum biyun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.