Kamfanonin DisCos Sun Yi Karin Haske a Kan Niyyar Lafta Kudin Lantarki Daga Shiga 2024

Kamfanonin DisCos Sun Yi Karin Haske a Kan Niyyar Lafta Kudin Lantarki Daga Shiga 2024

  • Har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga bangaren gwamnati da ta tabbatar da shirin karin kudin lantarki
  • Jami’an hukumar NERC ba su san da maganar canza farashin shan wuta ba duk da rade-radi suna ta yawo
  • Ma’aikatan kamfanonin DisCos sun shaida cewa ko akwai niyyar karin, gwamnati ba ta amince ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kamfanonin DisCos da ke da alhakin raba wutar lantarki a Najeriya sun musanya zancen yin karin kudi a shekarar nan.

Rahotanni sun zo cewa daga ranar 1 ga watan Junairu, 2024, kudin shan wuta zai tashi, Leadership ta kawo labari akasin haka.

Wutar lantarki
Babu niyyar karin kudin wutar lantarki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamfanonin sun tabbatar da cewa hukumar NERC mai kula da harkokin wuta ba ta bada umarnin karin farashi a halin yanzu ba.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DisCos za su kara farashin lantarki?

Punch ta tuntubi ma’aikatan kamfanonin DisCos akalla uku wanda su ka shaida mata babu wani gaskiya a rahoton karin kudin.

Wasu jami’an hukumar NERC da aka zanta da su, sun karyata rahoton da yake yawo, da alama gwamnati za ta cigaba da biyan tallafi.

Shugaban sadarwa na kamfanin Jos Electricity Distribution Company’, Adekole Elijah ya ce ba a bada umarnin karin kudin wuta ba.

Adekole Elijah ya ce ya ji jita-jita ta na yawo, amma babu wata takarda daga gwamnati da ta amince ayi karin kudin wutar lantarki.

Enugu DisCos sun ce babu karin kudin wuta

Emeka Ezeh wanda shi ne babban jami’in sadarwa a kamfanin rabon wuta na Enugu, yana cikin wadanda su ka karyata batun a jiya.

Shi ma Emeka Ezeh ya nuna har zuwa yanzu, NERC ba ta yarda da wani karin kudi ba ko da kamfanonin DisCos suna da niyyar yi.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Miyagu sun yi alkawarin sake kai hari bayan kashe mutum 195 a Filato

"Ba duka kudin wuta ake biya ba"

Wani ma’aikacin kamfanin Kaduna Electric ya shaida mana a yanzu kusan daya bisa ukun kudin wuta ake kawowa mutane su biya.

Ma’aikacin yake cewa ana yin haka ne saboda mutane su iya biyan bashinsu, ya nuna akwai yiwuwar nan gaba farashi ya canza.

Ana maganar wadanda su ke shan wuta ne ba tare da amfani da na'urar awo ba.

Kasafin kudin Majalisa a 2024

Idan aka koma kan kasafin kudin kasa, an ji labari 'yan majalisa da sanatoci za su kashe kudinsu a kai a shekarar 2024 da aka shiga.

Kusan N170bn za a kashe a ofisoshin ‘yan majalisa, hadiman ‘yan siyasan za su lakume N20bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel