Kudin wutan da ‘Yan Najeriya ke biya zai karu, Gwamnati ta yi na’am da karin farashi
- Hukumar da ke kula da harkar wuta a Najeriya ta ba kamfanonin DisCos dama su kara farashinsu
- Karin kudin zai fara aiki ne tun daga watan Fubrairun 2022 har zuwa karshen wannan shekarar
- NERC ta ce sauyin farashin da aka samu zai shafi kamfanonin JEDC, KEDCO, IKEDC, PHEDC da IBEDC
Abuja - Hukumar NERC mai kula da harkar wuta a Najeriya ta yarda wasu kamfanonin da ke da alhakin raba wuta da kara farashinsu a shekarar nan.
Rahoton da The Nation ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa a Junairun 2022 aka amince da karin farashin amma daga watan Fubrairu zai soma aiki.
Kamfanonin da aka yarda su kara kudin su ne: Port Harcourt Electricity Distribution Company (PHEDC); da Jos Electricity Distribution Company (JEDC).
Sai Kano Electricity Distribution Company (KEDC); Kaduna Electricity Distribution Company (KEDCO); da Ikeja Electricity Distribution Company (IKEDC).
Na karshe shi ne kamfanin Ibadan Electricity Distribution Company wanda aka fi sani da IBEDC.
Tsarin MYTO 2022
Sanarwar ta fito ne a wata takarda da ta fito daga hannun NERC wanda aka yi wa take da “This regulatory instrument shall be cited as Multi-Year Tariff Order (MYTO-2022) for Port Harcourt Electricity Distribution Company Plc (PHED”).

Asali: UGC
NERC ta kafa hujja da tashin farashin kaya, tsadar gas, da karyewar darajar Naira da karfin samar da lantarkin a matsayin dalilin da ya sa aka kawo karin.
Hukumar ta ce an yi la’akari da wasu alkaluma kafin a dauki wannan mataki. Dama a tsarin MYTO, duk bayan watanni shida za a rika duba farashin.
Jaridar The Cable ta ce shugaban NERC da mataimakinsa; Sanusi Garba da Musiliu Oseni sun sa hannu a tsarin na MYTO da aka kawo tun Disamban 2021.
Yadda karin zai kasance
Karin da aka samu yana nufin wadanda ke rukunin PHED (A-Non MD) da suke biyan N56.16/kwh a farkon shekarar 2022, za su koma biyan N60.67/kwh.
Haka zalika ‘yan rukunin PHED (B Non-MD) za su dawo biyan N59.64/kwh daga N56.64/kwh.
Rahoton ya ce wadanda ke kan layin E- MD2 za su daina biyan N50.72/kwh, za su koma biyan N54.22/kwh daga Fubrairu zuwa karshen shekarar bana.
Kudin waya zai karu
A makon nan rahoto ya zo mana cewa watakila mutane za su ga canji wajen kudin da ake kashewa yayin yin waya ko aika sakonni ta salula a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta amince a kara haraji a kan wasu kayan waya. Jami’an kwastam za su rika karbar 5% a matsayin kudin shiga.
Asali: Legit.ng