Gwamnatin Tinubu Za Ta Fitar da Naira Biliyan 600 Don Biyan Tallafin Wutar Lantarki a 2023

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fitar da Naira Biliyan 600 Don Biyan Tallafin Wutar Lantarki a 2023

  • Gwamnatin Shugaba Tinubu za ta kashe akalla Naira biliyan 600 wajen biyan tallafin wutar lantarki da 'yan Najeriya suka sha a 2023
  • Hakan na zuwa ne a gazawar gwamnati na cimma muradinta na rage kudin da take kashewa a tallafin wutar, inda a shekarar 2022 ta ware Naira biliyan 144
  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce Najeriya na aiki tukuru don samar da wasu hanyoyin samar da lantarki a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A lokacin da 'yan Najeriya ke kukan rashin wadatacciyar wuta, gwamnatin Tinubu na shirin fitar da Naira biliyan 600 don biyan kudin tallafin wutar lantarki a shekarar 2023.

Shugaban hukumar alkinta wutar lantarkin Najeriya Engr. Sanusi Garba ya sanar da hakan a wani taron tsare-tsaren samar da wutar lantarki da ya gudana a Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar magana: EFCC ta fara neman tsohon minista Agunloye ruwa a jallo, ta fadi dalili

Bola Ahmed Tinubu/Wutar Lantarki/Tallafi
Gwamnatin Tinubu ta shirya fitar da Naira biliyan 600 don biyan tallafin wutar lantarki a 2023. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Getty Images

Na wa Najeriya ke biya na tallafin wutar lantarki?

Garba ya ce gwamnatin ta yi kokarin rage kudin tallafin wutar lantarki daga Naira biliyan 528 zuwa Naira biliyan 144 a shekarar 2022, amma wannan shekarar, kudin sun karu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce babbar matsalar da fannin wutar lantarki ke samu shi ne rashin biyan kudin wuta da 'yan Najeriya ke yi, da rashin biyan harajin kamfanonin DisCo an kasar.

Ko a cikin watan Oktoba, sai da The Cable ta ruwaito gwamnati na cewa ta kashe Naira biliyan 171.25 wajen biyan tallafin wutar lantarki a watanni 6 na farkon shekarar 2023.

Gwamnati ta nemo hanyar magance matsalar wutar lantarki

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce akwai bukatar samar da wani kamfani daga kamfanin TCN da zai taimaka wajen bukasa rarraba wutar lantarki da samar da ita.

Kara karanta wannan

Cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa a karo na uku

Adelabu ya ce rashin ingantattun kayan ayyuka a kamfanin TCN ya sa kamfanin ba ya iya samar da wutar da za ta ishi amfanin 'yan Najeriya, rahoton Daily Trust.

Ya kuma tabbatar da kokarin gwamnati na yin amfani da wasu hanyoyin samar da lantarki a kasar da suka hada da hasken rana, iska, da sauran makamashi don wadatar da wutar a Najeriya.

Cibiyar samar da wutar lantarki ta durkushe, karo na uku a 2023

A wannan makon ne muka kawo maku labarin yadda cibiyar wutar lantarkin Najeriya ta sake durkushewa, wanda ya tilasta daukewar wuta a Najeriya.

Karo na uku kenan cibiyar na durkushewa, inda ko a watan Satumbar wannan shekarar sai da cibiyar ta durkushe har sau biyu amma ana gyarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel