Gwamna Adeleke: “Burina Shi Ne in Zama Mawaki Kamar Davido, Ba Wai Dan Siyasa Ba”

Gwamna Adeleke: “Burina Shi Ne in Zama Mawaki Kamar Davido, Ba Wai Dan Siyasa Ba”

  • Za mu iya cewa kaddarar rayuwa ta sauya wa Ademola Adeleke wanda ya yi burin zama mawaki amma a karshe ya zama gwamnan jihar Osun
  • A cewar Gwamna Adeleke, tun a shekarun 1980 ya so zama mawaki, amma mahaifinsa ya ki amincewa inda ya tura shi makaranta har zuwa Amurka
  • Adeleke ya yi nuni da cewa baiwar rawarsa da waka ce ya mika wa dan uwansa Davido da kuma dansa, amma har yanzu yana sha'awar nishadi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ba da labarin yadda mahaifinsa ya cire masa son sha'awar zama mawaki.

Ya ce shi burinsa shi ne ya zama mawaki ko kuma dai wani mai taka rawa a masana'antar nishadi, ba wai ya zama dan siyasa ba.

Kara karanta wannan

"Yadda mutum zai yi kudi bayan ya isa Canada": Matashi da ke zaune a Turai ya yi muhimmin bayani

Gwamna Adeleke tare da mawaki Davido
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce burinsa ya zama mawaki ba wai dan siyasa ba. Hoto: @AAdeleke_01
Asali: Twitter

Adeleke, saboda son rawarsa, aka yi masa lakani da "gwamnan rawa", wanda bidiyoyin da suka nuna shi yana rawa sun karade shafukan sada zumunta, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda na so zama mawaki amma mahaifina ya hana - Adeleke

Gwamnan wanda kuma dan uwana ne ga mawaki Davido ya sha suka kan yadda ya ke tikar rawa yayin yakin neman zabe, inda wasu ke ganin bai cancanci zama gwamnan jihar Osun ba.

Adeleke ya ce:

"Ni burina shi ne na zama mawaki, amma mahaifina bai amince da wannan kudiri ba. Mutanen da ba sa kallon waka matsayin sana'a, su dai burinsu ka tafi makaranta.
"Ina ga wannan basirar da baiwar ta wa ce na ba dan uwana Davido da kuma yaron ciki na. Ma damar za ka kunna waka, to ba na sanin lokacin da zan fara taka rawa."

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

Gwamna Adeleke ya ce a shekarar 1981 ya je Amurka yin karatu a Alabama, jami'ar jihar Jacksonville, lokacin da za a yi bikin shekarar makaranta, ya zabi fannin rawa, har ya kai matakin karshe.

"In takaita maku labari, ni ne na lashe wannan gasar rawar, zan iya tunawa, shugaban makarantar ya kirani da 'Jackson' lokacin da ya ke kokarin kiran sunana Ademola Adeleke."

Adeleke ya ce tun daga wannan lokaci ne sunan Jackson ya bi shi, domin lokacin dan rawa kuma mawaki Michael Jackson yana ganiyar tashensa.

Gwamna Adeleke ya dawo Najeriya, ya karyata masu jita-jita

A wani labarin, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki 30 a kasar waje yana hutawa, lamarin da wasu ke jita-jitar ya je neman magani ne.

Sai dai dawowar Adeleke ta diga aya kan masu jita-jitar, inda ya ce ya je kasar waje don ya huta kawai, kuma lafiyar kalau, sabanin yadda wasu ke cewa ba zai iya shugabanci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel