Wasu sun maka Sakataren Gwamnatin ‘Yar’adua a gaban kotu a kan saida masu kadarori

Wasu sun maka Sakataren Gwamnatin ‘Yar’adua a gaban kotu a kan saida masu kadarori

  • Masu hannun jari a kamfanin inshoran Industrial and General Insurance Plc sun shigar da kara a kotu
  • Wadannan mutane su na zargin su Mahmud Yayale Ahmed da saida kadarorin kamfanin babu izninsu
  • Yayale Ahmad yana cikin masu sa ido a aikin kamfanin da ake zargin sun yi shekara 5 ba su zauna ba

Lagos - Wasu daga cikin masu hannun jari a kamfanin inshora na Industrial & General Insurance Plc, sun yi karar tsohon sakataren gwamnatin tarayya a kotu.

A ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba, 2021, Punch tace wadannan mutane sun maka Alhaji Mahmud Yayale Ahmed a gaban kotun tarayya da ke Legas.

Jaridar tace masu hannun jari a kamfanin na Industrial and General Insurance Plc su na zargin Mahmud Yayale Ahmed da wasu mutane bakwai da saba doka.

Kara karanta wannan

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

Ana zargin tsohon sakataren gwamnatin da sauran mutanen da shafe sama da shekara biyar ba tare da sun kira taron da ya kamata a yi a duk shekara-shekara ba.

Baya ga haka, masu rike da hannun jarin sun ce ‘yan majalisar masu kula da kamfanin su na ta saida wasu kadarorinsu, ba tare da sun samu amincewar su ba.

Sakataren Gwamnatin ‘Yar’adua
Mahmud Yayale Ahmad da 'Yar'adua Hoto: @Northeast-Reporters
Asali: Facebook

Zargin da ke kan su Yayale Ahmed

Ganin yadda ake karkatar ko saida kadarorin kamfanin inshoran, kauyoyin wadanda suka shigar da kara sun ce an saba dokar kula da kamfanoni ta shekarar 2020.

Lauyoyin sun bukaci kotu ta haramtawa Alhaji Yayale Ahmad da sauran ‘yan majalisarsa alaka da kamfanin saboda sun gaza kiran zamansu na shekera-shekara.

Baya ga haka, rahoton yace ana tuhumarsu da kin bayyana yadda kamfanin yake kashe kudi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna

Wadanda za su kare kansu a kotu

Sauran wadanda ake tuhuma a babban kotun a wannan shari’a mai lamba ta FHC/L/CP/1699/2021 sun hada da manajan kamfanin kansa, Mista Rachel Emenike.

Sai kuma Farfesa Oladapo Afolabi; Augustine Olorunsola; Kanayo Okoye; Gafar Animashaun da Abiodun Ajifolawe. Ana sauraron ranar da za a fara sauraron shari'ar.

Ummarun Kwabo zai zama surukin Sarki Aminu Ado Bayero

A karshen makon jiya aka ji babban 'dan Sarkin Kano, Kabiru Bayero zai auri ‘diyar mashahurin attajiri kuma ‘dan kasuwar garin Sokoto, Alhaji Ummarun Kwabo.

Tawagar Sarakunan Bichi da na Kano sun nemi auren Aisha Ummarun Kwabo kumar har an biya N250, 000 a matsayin sadakin auren a gidan gwamnan jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel