Michael Jackson: Duk da cewa ya shekara 10 da mutuwa amma har yanzu shine tauraron mawaka da yafi kowa daukar albashi a shekarar 2019

Michael Jackson: Duk da cewa ya shekara 10 da mutuwa amma har yanzu shine tauraron mawaka da yafi kowa daukar albashi a shekarar 2019

- Marigayi kuma tsohon mashahurin mawakin nan na duniya Michael Jackson ya zama na daya a cikin jerin taurarin mawaka da suka fi daukar kudi a duniya

- Mawakin ya zama na dayan ne bayan ya samu kudi kimanin dalar Amurka miliyan sittin

- Wanda ya biye mishi shine tsohon mawaki Elvis, wanda ya samu dalar Amurka miliyan talatin da tara

Sarkin mawakan Pop na duniya, Michael Jackson, wanda ya mutu a shekarar 2009 bayan ya kashe kanshi ta hanyar shan miyagun kwayoyi da suka yi sanadiyyar ajalinsa, yanzu haka dai ya fito a matsayin tauraro na daya da suka mutu da ya fi kowa daukar kudi a karo na bakwai a jere, inda ya samu dala miliyan sitti ($60m) a watan Oktobar shekarar 2018.

A cikin jerin sunayen mawakan da suka mutu da aka wallafa wannan satin, Michael Jackson ya samu karin masu kallo da sauraron wakar shi inda suka kai mutane biliyan biyu da digo daya (2.1b) a kasar Amurka, yayin da a da yake da mutane biliyan daya da digo takwas (1.8b).

Haka ita ma tsohuwar mawakiyar nan 'yar kasar Amurka, Nipsey Hussle, wacce aka harbeta ranar 31 ga watan Maris, ita ma ta samu damar shiga cikin jerin wadannan mutanen inda ta zo a matsayin ta 10 da kudi dala miliyan goma sha daya ($11m).

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda aka nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana rakashewa a wajen wani biki

Kamar dai yadda aka ruwaito Michael Jackson yana samun yawancin kudin shi a bangaren waka ne. Haka kuma yana da wani kamfani na kayan sawa mai suna Marathon Clothing, a lokacin da yake raye, duk da dai an san yawan kudin da kamfanin kayan nashi yake kawo masa, amma ya taimaka wajen karuwar kudin shi a watanni sha biyu da suka gabata.

Ga dai jerin taurarin wadanda suka mutu da kuma kudin da suke samu.

1. Michael Jackson - $60m

2. Elvis - $39m

3. Charles Schultz - $38m

4. Arnold Palmer - $30m

5. Bob Marley - $20m

6. Dr. Seuss - $19m

7. John Lennon - $14m

8. Marilyn Monroe - $13m

9. Prince - $12m

10. Nipsey Hussle - $11m

11. XXXtentacion - $10m

12. Whitney Houston - $9.5m

13. George Harrison - $9m

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel