Kasafin Kudi: Biliyoyin da Kowane Gwamna Yake Niyyar Kashewa a Shekarar 2024

Kasafin Kudi: Biliyoyin da Kowane Gwamna Yake Niyyar Kashewa a Shekarar 2024

  • Gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi sun kammala aiki a kan kudin da za su kashe a shekara mai zuwa
  • Kasafin kudin ya kai gaban ‘yan majalisar tarayya da na dokoki a jihohi, a wasu wurare har an amince da su
  • Akwai Gwamnonin da sun sa hannu a kundin kasafin 2024, an san abin da jihohinsu za su batar a badi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Rahoton nan ya tattaro bayanan kudin da ake sa ran shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni za su kashe a 2024.

A shekarar da za a shiga gwamnatin tarayya tayi kasafin N27.50tr wanda akwai yiwuwar ‘yan majalisar tarayya su kara kudin.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya ya lissafo jihohin da talauci, wahala da rashin tsaro za su karu a 2024

Kasafin kudin Jihohi
Kasafin kudin Jihohi da Gwamnatin Tarayya a 2024 Hoto: @KYusufAbba, @jidesanwoolu, @HonBago
Asali: Twitter

Kasafin kudin kowane yanki a 2024

Idan aka koma ga jihohi, gwamnonin Kudu maso yamma za su kashe N4.2tr, na Kudu maso kudu sun yi kasafin N3.43tr a badi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin da ke jihohin Arewa maso yamma za su kashe N2.5tr, sai na Kudu maso gabas za su batar da N2.29tr a shekarar 2024.

Kasafin kudin jihohin Arewa ta tsakiya shi ne N1.89tr sai a kashe N1.60tr a Arewa maso gabas wanda shi ne mafi karanci.

Yadda jihohi za su batar da kudi

StatiSense ta tattaro kasafin kudin jihohi 36 da ake da su kuma za a fahimci Legas ce a kan gaba da ta ke shirin kashe tiriliyoyi.

Daga Kudu akwai Akwa Ibom, Ogun, Delta, Imo, Ribas, Bayelsa da Enugu su na cikin jihohi masu kasafin kudi mai yawa a 2024.

Ba a bar irinsu Neja a baya ba wanda gwamna Umar Bango ya gabatar da kasafin N613bn sai Kaduna, Katsina, Kano da Zamfara.

Kara karanta wannan

Abin da shugaba Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Legas

Nawa gwamnoni za su kashe?

1. Abia: ₦567.20bn

2. Adamawa: ₦225.89bn

3. Akwa Ibom: ₦845.63bn

4. Anambra: ₦410.10bn

5. Bauchi: ₦300.22bn

6. Bayelsa: ₦480.99bn

7. Benuwai: ₦225.73bn

8. Borno: ₦340.62bn

9. Kuros Riba: ₦250bn

10. Delta: ₦724.90bn

11. Ebonyi: ₦202.13bn

12. Edo: ₦325.30bn

13. Ekiti: ₦159.57bn

14. Enugu: ₦521.56bn

15. Gombe: ₦207.75bn

16. Imo: ₦592.23bn 17

17. Jigawa: ₦298.14bn

18. Kaduna: ₦458.27bn

19. Kano: ₦350.20bn

20. Katsina: ₦454.31bn

21. Kebbi: ₦250.13bn

22. Kogi: ₦258.28bn

23. Kwara: ₦286.40bn

24. Legas: ₦2.25tn

25. Nasarawa: ₦199.88bn

26. Neja: ₦613.27bb

27. Ogun: ₦703.03bn

28. Ondo: ₦384.53bn

29. Osun: ₦273.91bn

30. Oyo: ₦434.22bn

31. Filato: ₦295.43bn

32. Ribas: ₦800.39bn

33. Sokoto: ₦270.10bn

34. Taraba: ₦311.39bn

35. Yobe: ₦217.00bn

36. Zamfara: ₦423.52bn

Kasafin kudin Bola Tinubu a 2024

Ana da labari Majalisar tarayya tana fatan a kammala zama a kan kundin kasafin kudin 2024 kafin karshen shekarar bana

Sanata Opeyemi Micheal Bamidele ya ce ‘yan majalisa da Sanatoci sun kusa gama aiki, a amince da kasafin kudin na 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel