NLC: Tuni El-Rufai Ya Koma Biyan N18,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi
- Kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna ta zargi gwamnatin El-Rufai da zaftare albashin wasu ma'aikata
- Kungiyar ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta koma biyan N18,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata
- Hakazalika ta yi zargin cewa gwamnati na shirin tura 'yan daba don lalata zanga-zangar lumana da suke yi
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a jiya ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna na shirin kutsa kai cikin zanga-zangarta tare da tura ‘yan daba, The Nation ta ruwaito.
Sanarwar ta ce an yaudaru ne wajen yaba wa gwamnatin Nasir El-Rufai saboda kasancewa ta farko da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin N30,000.
NLC, a cikin wata sanarwa ta bakin Shugabanta na Majalisar Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman, ya ce tun tuni jihar ta sake komawa ga tsohon tsarin albashin N18, 000 ga wasu ma’aikatan.
Ya ce ma'aikatan gwamnati dubu 20 suna karbar rabin albashi kasa da N18, 000.
KU KARANTA: Dawo-dawo: Matasan Najeriya Sun Kudiri Aniyar Tarawa Jonathan Kudin Takara a 2023
Kungiyar ma’aikatan ta ce mambobinta na bin jihar bashin alawus da dama.
Ta yi Allah wadai da barazanar kama Shugaban NLC, Ayuba Wabba.
“Muna jan hankalin jama’a ga shirin tattara 'yan daba da gwamnatin jihar ke yi don lalata na zanga-zangar mu ta lumana. Muna kira ga mutanen jihar Kaduna da su yi taka tsantsan su tsaya kan wannan shirin.
“Muna rokon jama’a da su kasance cikin nutsuwa da lumana a tsawon yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
“Muna tabbatar wa ma’aikatan jihar Kaduna da sauran jama’ar gari cewa za mu ci gaba da gudanar da yajin aikin cikin lumana don biyan bukatunsu,” in ji Suleiman.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya Sun Ragargaji Boko Haram Da Bama-Bamai a Borno
A wani labarin, Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, a ranar Lahadi ya karbi bakuncin daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya dake Kaduna, wadanda kwanan nan suka samu 'yanci daga hannun 'yan bindiga.
A ranar 12 ga watan Maris, 'yan bindiga sun mamaye makarantar da ke kan titin filin jirgin sama a Kaduna suka yi awon gaba da dalibai 39. An saki goma daga cikinsu bayan rahotanni sun nuna cewa iyayensu sun biya kudin fansa naira miliyan 17, TheCable ta ruwaito.
Ragowar daliban 29 sun samun 'yanci a ranar 5 ga watan Mayu bayan sun kwashe kwanaki 54 a tsare.
Asali: Legit.ng