Yadda Abba Gida-Gida Ya Samu Matsala, Aka Yi Laifi Wajen Yin Rusau a Jihar Kano

Yadda Abba Gida-Gida Ya Samu Matsala, Aka Yi Laifi Wajen Yin Rusau a Jihar Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya ruguza shaguna da gidajen da aka gina a cikin watan farko da ya shiga ofis a jihar Kano
  • Wasu lauyoyi sun ce abin da gwamnan ya yi ya saba doka, babu mamaki shiyasa kotu ta same shi da laifi
  • Gwamna Abba ya sasanta da wasu ‘yan kasuwa da su ka kai ta kotu, aka ci gwamnatin Kano tarar N30bn

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A ranar 3 ga watan Yuni, Mai girma Abba Kabir Yusuf ya bada umarni a ruguza shaguna 90 da ke filin sukuwa a jihar Kano.

Wannan umarni da wasu da Gwamnan jihar Kano ya bada jim kadan bayan hawansa mulki ya sabawa dokoki inji Premium Times.

Kara karanta wannan

An bankado likitocin da suka tsere kasashen waje da ke cigaba da karbar albashi a Najeriya

Abba Rusau
Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi rusau Hoto: Hoto: @KysufAbba/@Imranmuhdz (X)
Asali: Twitter

Ra'ayin lauyoyi a kan Rusau a Kano

Lauyoyi sun bayyana cewa akwai wasu ka’idoji da ake bi kafin a ruguza ginin mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masana da su ka yi magana da jaridar sun ce gwamna yana da damar karbe filaye idan an saba ka’ida, amma akwai matakai da ake bi.

Sashe na 28(6) na dokar kasa ta halattawa gwamna wannan, amma Barista Mustapha Kashim ya ce sai an sanar da masu filayen.

Lauyan yake cewa sai gwamnati ta ba mai fili isasshen lokaci kafin a tada shi ko a rusa masa dukiya, yin akasin hakan zai zama laifi.

Shari'ar Rusau kafin zuwan Abba a tarihi

Shari’ar NITEL da wani Ogunbiyi (a 1992) a kotu ta tabbatar dokar kasa ba ta amince a kori mutum daga filinsa ba tare da sanar da shi ba.

Zuwa da motoci cikin dare ya sabawa ka’ida, Kashim ya ce kotun koli tayi tir da irin haka a 1986 a shari’ar gwamnatin Legas da Ojukwu.

Kara karanta wannan

Sabon rikici zai kurdo jam’iyyar PDP, Atiku ya lula Dubai bayan shari’ar zabe

Nasiru Aliyu Farfesan shari’a ne a jami’ar Bayero a Kano, ya ce akwai ka’idoji da dole a bi wajen karbe filin da aka mallaka ba bisa ka’ida ba.

Farfesa Nasiru Aliyu ya ce sai an sanar da mai filin, kuma yana da damar zuwa kotu, Alkalai ne za su raba gardamar halaccin kadarar.

"Za su rusa mana gida"

Legit ta zanta da wani ‘dan kasuwa mazaunin Kano, ya fada mana gwamnati ta yi alama a shagonsu da nufin za a ruguza wurin.

Watanni kusan biyar kenan da gwamnati ta nuna za ta rusa shagunan da gidajen wanka a yankin ‘Court road’, amma ba a aiwatar ba.

‘Dan kasuwan ya ce suna ta addu’o'i Allah SWT ya tsare dukiyarsu daga rushe-rushen kamar yadda hakan ya shafi wasu mutanen.

Rushe-rushen Gwamnatin Abba a Kano

Ana da labari gwamna Abba Kabir Yusuf ya rusa gine-gine irinsu otel na Daula, shaguna a Kantin Kwari da shaguna da ke masallacin idi.

Bayan haka, gwamnatin jihar Kano ta rusa gidaje a Salanta da sunan sun sabawa doka. Sai dai wa'adin da ake badawa na 'yan kwanaki ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel