An Bankado Likitocin Da Suka Tsere Kasashen Waje Da Ke Cigaba Da Karbar Albashi a Najeriya

An Bankado Likitocin Da Suka Tsere Kasashen Waje Da Ke Cigaba Da Karbar Albashi a Najeriya

  • Gwamnatin jihar Abia ta ce ta gano wasu likitoci da suka ajiye aiki amma har yanzu suna karbar albashi daga gwamnatin jihar
  • Mai girma Gwamna Alex Otti ya ce mafi yawan likitocin sun tsere zuwa kasashen waje neman abin duniya amma suke ci gaba da karbar albashi
  • Gwamnan ya ce ba zai kyale wannan cin amanar ba, don haka dole hukumomin da abin ya shafa su dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Abia - Mai girma Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ce ya gano wasu likitoci da gwamnatin jiharsa ke biya albashi duk da sun tsere sun koma aiki a kasashen waje.

Otti ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi a wani taron majalisar kiwon lafiya ta jihar a ranar Alhamis a Umahia inda ya ce likitocin na karbar albashi duk da sun san sun ajiye aiki.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya ware naira biliyan 15.97 don yin wasu manyan ayyuka 2 a kwaryar jihar Kano

Likitocin Najeriya na zuwa turai ci-rani
Gwamnatin Abia ta bankado likitocin da suka tsere kasashen waje da ke cigaba da karbar albashi a Najeriya. Hoto: Getty Images. (A kula: Wanda ke jikin hoton bai da alaka da labarin)
Asali: Getty Images

The Punch ta ruwaito gwamnan na nuni da cewa tafiya ci-rani da likitoci ke yi zuwa kasashen ketare ya jawo koma baya a fannin lafiyar jihar, ya kuma yi alkawarin inganta albashi da walwalar likitoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin da gwamnati za ta dauka kan likitoci masu zuwa ci-rani

Ya ce:

"Mun yanke shawarar biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya da wuri, da kuma bunkasa walwalarsu don kawo karshen zuwa ci-rani da suke yi kasashen waje."

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kara daukar wasu ma'aikatan kiwon lafiya don bunkasa fannin lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce:

"A shirinmu na mayar da tsarin aikin gwamnati zuwa na zamani a jihar Abia, mun gano wasu likitoci da har yanzu suke karbar albashi duk da sun ajiye aikin, sun tafi turai ci-rani.
"Wannan laifi ne da dole hukumomin da abin ya shafa za su dauki mataki, abin da yanzu muka mayar da hankali kansa shi ne kara yawan likitoci da bunkasa rayuwarsu."

Kara karanta wannan

Abin da ya sa likitoci ba sa zama a asabitocin jihar Kogi, CMD ya yi karin bayani

Ministan ilimi, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Abia, Dr. Ifenyiwa Uma-Kalu, ya ce akwai bukatar jihohi su samar da gine-ginen cibiyoyin kiwon lafiya.

Abin da ya sa likitoci ba sa zama a asibitin jihar Kogi

Hukumar gudanarwar asibitin kwararru na jihar Kogi ta sanar da cewa har yanzu likitoci ba sa neman aiki a asibitin duk da bude kofar da suka yi.

A cewar Dr. Ish Adagiri, ya ce likitoci na ajiye ayyukansu a Najeriya suna tsallakewa zuwa kasashen ketare don yin aiki da zummar tara makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel