Zargin Cin Hanci: Gwamnatin Kano Ta Canza Kotun da Ake Shari’ar Ganduje da Iyalansa

Zargin Cin Hanci: Gwamnatin Kano Ta Canza Kotun da Ake Shari’ar Ganduje da Iyalansa

  • Babbar mai shari'a ta jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta sauya kotun da za ta saurari shari'ar gwamnatin jihar da Abdullahi Ganduje
  • Gwamnatin Kano na tuhumar tsohon gwamna Ganduje, iyalinsa da wasu mutane da laifin almubazzaranci da kudin jama'a
  • A yayin da gwamnati ta shirya shaidu 12, an dage shari'ar daga kotun Malam Na’abba zuwa kotun Mai shari’a Amina Adamu Aliyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano - Babbar mai shari’a kuma kwamishinar shari’a ta Kano, Dije Abdu Aboki, ta sauya kotun da za ta saurari shari’ar da ake yi tsakanin Gwamnatin jihar da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Niger: An kama Yara 15 cikin mutane 30 da ke hakar ma'adanai ta haramtacciyar hanya

Bayan shari’ar Dr. Abdullahi Ganduje, mai shari’a Dije ta kuma sauya kotun da za su saurari wasu karin shari’a guda bakwai.

Abdullahio Ganduje
Ma'aikatar shari'a ta sauya kotun da ke sauraron shari'ar Abdullahi Ganduje Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Daily trust ta wallafa cewa hakan na nufin an dauke shari’ar Abdullahi Umar Ganduje daga gaban babbar kotu mai zamanta a Audu bako karkashin mai shari’a Malam Na’abba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma mayar da ita zuwa kotu mai lamba bakwai da ke zamanta a Miller road karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu.

Ma’aikatar shari’a na iya sauya kotu

Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar shari’a da ke jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya bayyana cewa su na da ikon sauya kotu a kan shari’ar da su ka ga ya kamata.

Ya ce doka ta ba su damar yin hakan matukar shari’ar ba ta kai matakin yanke hukunci ba, kamar da wacce ake yi tsakanin gwamnati da Dr. Ganduje.

Kara karanta wannan

Daurarru sun shaki iskar ’yanci da Gwamnatin Kano ta yiwa fursunoni Afuwa

Solace base ta tattaro cewa Gwamnatin jihar Kano dai na tuhumar tsohon Gwamnan jihar, kuma shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa, dansa da wasu mutane biyar da almubazzaranci da kudin jama’a.

Gwamnati za ta gabatar da shaidu guda 15 gaban kotun yayin zaman da za a fara idan ta sanya lokacin fara shari'ar.

Kotu ta dakatar da binciken Dr. Ganduje

Mun ba ku labarin cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta haramtawa kwamitocin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya kafa daga binciken shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari’a Simon Amobeda ne ya umarci kwamitocin su dakata har sai an kammala sauraron da Dr. Ganduje ya shigar gabansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel