"Ba Buhari Bane" An Gano Wanda Ya Sa Tsohon Gwamnan CBN Ya Canza Takardun Naira a Najeriya

"Ba Buhari Bane" An Gano Wanda Ya Sa Tsohon Gwamnan CBN Ya Canza Takardun Naira a Najeriya

  • Ana zargin tsohon gwamnan babban banki (CBN), Godwin Emefiele, da canza takardun Naira ba tare za amincewar Muhammadu Buhari ba
  • Jim Obazee, mai binciken CBN mai zaman kansa wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ne ya bayyana haka a rahotonsa
  • A cewar rahoton, Emefiele ya haɗa baki ne da Sabi'u Tunde, hadimi kuma ɗan ɗan-uwan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bincike kan yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya tafiyar da harkokin CBN na ƙara bayyana musamman kan tsarin canza Naira.

Wata gaskiya mai kaɗa hanji daga cikin rahoton binciken ta nuna cewa Emefiele ya canza N200, N500 da N1000 ba tare da amincewar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

"An fara ruwan kuɗi" Gwamnatin Tinubu ta fitar da sabuwar sanarwa kan biyan kuɗin N-Power

Shugaba Tinubu da tsohon gwamnan CBN.
"Ba Buhari Bane": Bincike Ta Tona Wanda Ya Bada Umarnin Canza Naira a Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Haka nan kuma ana zargin tsohon gwamnan CBN ɗin da baiwa wani kamfani a Burtaniya aikin buga sabbin kuɗin kan N61.5bn wanda ya saɓa wa umarnin Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano cewa Muhammadu Buhari ya bada umarnin buga sabbin kuɗin a Najeriya amma Emefiele ya yi gaban kansa ya ba kamfanin De La Rue aikin.

Wanda aka ba aikin binciken CBN ya miƙa rahoto ga Tinubu

A cewar rahoton Punch, Jim Obazee, wanda ya gudanar da bincike bayan shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi, ya gano cewa tun asali ba Buhari ya bada umarnin canza kuɗi ba.

A rahoton da ya miƙa, ya ce amincewa da canza takardun N200, N500 da N1000 ya fito ne daga Tunde Sabiu Yusuf, hadimin Buhari, shugaban ƙasa a wancan lokacin.

Duk wannan na cikin rahoton karshe da Jim Obazee ya miƙa wa Tinubu ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023 mai taken, "Rahoton Bincike na musamman kan CBN da abubuwan da ke da alaƙa."

Kara karanta wannan

Binciken da aka yi a CBN ya bankado abubuwan da Emefiele ya aikata lokacin Buhari

Rahoton binciken ya yi bayani baro-ɓaro cewa Emefiele ya haɗa baki da Tunde suka aiwatar da tsarin sauya takardun kuɗin.

Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Gidan Gwamnatin Jihar PDP

A wani rahoton na daban Shiga tsakanin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a rikicin jihar Ribas ya bar baya da ƙura.

Ɗaruruwan masu zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal ranar Jumu'a domin nuna adawa da yarjejeniya 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel