Murna Yayin da Matatar Mai Ta Fara Aiki a Najeriya, Za Ta Fafata da Ta Dangote da Saura

Murna Yayin da Matatar Mai Ta Fara Aiki a Najeriya, Za Ta Fafata da Ta Dangote da Saura

  • Ana cikin murna a Najeriya bayan fara aiki a matatar Port Harcout da ke jihar River da ke Kudancin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin cewa matatar za ta fara aiki a Disamba
  • Ana sa ran matatar za ta rinka fitar da ganga dubu 210 a ko wace rana wanda zai kara kawo gasa a tsakanin matatun mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Bayan daukar lokaci ana dakon fara aikin matatar man Port Harcout, a karshe buri ya cika.

Matatar ta Port Harcourt ta fara aiki inda ta tabbatar da alkawarin Gwamnatin Tarayya na fara aikin a watan Disamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi magana mai muhimmanci bayan matatar mai ta Port Harcourt ta fara aiki

Ana cikin murna yayin da matatar mai ta fara aiki a Najeriya
Matatar mai Port Harcourt ta fara aiki a Najeriya. Hoto: NNPC.
Asali: UGC

Yaushe aka sanar da fara aikin matatar?

A cikin wani faifan bidiyo, an kunna wutar matatar a jiya Laraba 20 ga watan Disamba wadda ke nuna fara aikin matatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon wanda ya aka wallafa a shafin X ya ce kunna wutar na nuna tabbacin fara aikin matatar a kasar.

Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya yi alkawarin fara aikin matatar a watan Disamba.

Wane tabbaci Kyari ya bayar kan matatar mai din?

Har ila yau, Shugaban kamfanin man NNPCL, Mele Kyari ya tabbatar da cewa za a dai na shigo da mai zuwa karshen wannan wata.

Ya kuma tabbatar da cewa fara aikin matatar mai din zai kawo gasa tsakanin 'yan kasuwa wanda zai jawo sauki a harkar dillancin mai din.

Kara karanta wannan

Masanin tattalin arziki ya yi jasashen abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2024

Kyari ya ce:

"Ina mai tabbatar muku da cewa zuwa karshen watan Disamba za mu fara aiki a matatar Port Harcourt.
"Farkon shekarar 2024 matatar Warri za ta fara aiki yayin da a karshen shekarar 2024 ta Kaduna za ta dauki harama."

Bashin Najeriya ya kai tiriliyan 87

A wani labarin, Hukumar Kula da Basuka a Najeriya, DMO ta tabbatar da yawan basukan da ake bin Najeriya a halin yanzu.

Hukumar ta ce an kididdiga yawan basukan ne zuwa karshen watan Satumbar wannan shekara.

Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Tinubu ya sake neman sahalewar Majalisa don karbo bashin a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel