Dalar Amurka Ta Kara Yin Raga Raga da Naira a Kasuwar Musayar Kuɗi a Najeriya

Dalar Amurka Ta Kara Yin Raga Raga da Naira a Kasuwar Musayar Kuɗi a Najeriya

  • Duk da natakan da CBN ke ikirarin ɗauka, ƙimar Naira na ci gaba da yin ƙasa a kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage a Najeriya
  • A ranar Laraba, ƴan canji sun sayi kowace Dala kan N1,410 kuma su sayar wa kwantomomi kan N1,450 watau suna cin ribar N40
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan CBN ya ƙayyade iyakar kuɗaɗen da kamfanonin mai za su rika turawa kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, 2024, ƙimar Naira ta ƙara faɗuwa kan Dalar Amurka yayin da ta dawo N1z450/$ a kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage.

Wannan faɗuwa da Naira ta sake yi ya jawo raguwar kashi 1.4% daga farashin N1,430 da aka yi hada-hada da shi ranar Litinin, 6 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

An ƙara yi wa dakarun sojoji sama da 20 kisan gilla a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Naira ta kara faɗuwa.
Dalar Amurka ta ƙara tashi a kasuwar musayar kuɗi ta bayan fage Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Naira ta karye a kan Dala yau

Masu hada-hadar musayar kuɗi waɗanda aka fi sani da ƴan canji suna sayen kowace Dala ɗaya kan N1,410 kuma suna sayar wa kwastomomi kan N1,450.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Cable ta tattaro, ƴan canjin suna bin ribar N40 a kan kowace Dalar Amurka da suka saya kuma suka sayar.

Haka nan kuma a kasuwar hukuma, darajar kudin gida Najeriya ta ragu da kashi 1.98% zuwa N1,421.06 a ranar 8 ga Mayu daga N1,416.57/$ na ranar 7 ga Mayu.

Yayin hada-hadar ta ranar Laraba, mafi ƙoluluwar tashin Dala shi ne N1,440 yayin kuma farashin kuɗin Amurka bai yi ƙasa da N1,335 ba, rahoton This Day.

CBN da matakan farfado Naira kan Dala

A ranar 7 ga Mayu, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake nazari kan umarnin da ya bayar game da kudaden da kamfanonin mai na kasa da kasa (IOCs) ke fitarwa zuwa kasashen waje.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama 'yan canji 17 a kasuwar musayar kuɗi a jihar Kano

Tun da farko a watan Fabrairu, CBN ya gindaya iyaka a musayar kudaden da IOCs ke fitarwa zuwa asusun iyayen kamfanonin na ketare a wani bangare na shawo kan dukan da Naira ke she a hannun Dala.

EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika

A wani rahoton kuma, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ɗiyarsa Fatima sun isa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Hukumar EFCC ta shirya gurfanar da tsohon ministan, ɗiyarsa, surukinsa da wani kamfani a gaban mai shari'a kan yadda aka yi da wasu kuɗin kwangila N2.7bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel