Garabasa: Farashin rijistar kamfanonin kasuwanci ya koma N5,000 a hukumar CAC

Garabasa: Farashin rijistar kamfanonin kasuwanci ya koma N5,000 a hukumar CAC

- Hukumar dake rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci ta Najeriya, ta sanar da rage farashin yin rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci daga N10,000 zuwa N5,000

- Hukumar ta kuma ce adana sunan kamfanin kasuwanci zai kasance akan N500 har zuwa 31 ga watan Maris

- CAC ta ce wannan garabasa ce don baiwa daukacin al'umma mallakar asusun bankuna na kamfanoni damar karbar bashi, da kuma sauran tallafi daga gwamnati

Hukumar dake rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commission (CAC) ta sanar da rage farashin yin rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci daga N10,000 zuwa N5,000, wanda ke nuni da ragin kaso 50.

Hukumar ta kuma ce adana sunan kamfanin kasuwanci zai kasance akan N500 har zuwa 31 ga watan Maris.

A cikin wata sanarwa a shafinta na Twitter da ta fitar ranar Alhamis, hukumar CAC ta ce wannan garabasa ce don baiwa daukacin al'umma mallakar asusun bankuna na kamfanoni damar karbar bashi, da kuma sauran tallafi daga gwamnati

KARANTA WANNNAN: Nafisa Abdullahi: Dalilin da ya sa na daina soyayya da Adam A Zango

Garabasa: Yan kasuwa zasu koma biyan N5,000 na rijista da hukumar CAC
Garabasa: Yan kasuwa zasu koma biyan N5,000 na rijista da hukumar CAC
Asali: Twitter

"A kokarinta na kara bunkasa ayyukanta, hukumar dake rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commission (CAC) rage farashin yin rijistar sunayen masana'antu na kasuwanci daga N10,000 zuwa N5,000.

"Haka zalika, adana sunan kasuwanci zai kasance akan N500, wanda zai ci gaba da kasancewa a haka har zuwa 31 ga watan Disamba, 2018.

"Manufar yin hakan shine samar da wani tsari da ke da nasaba da bude kofa ka bankunan kasuwanci, kanana da matsakaitun masana'antu (MSMEs), da nufin bunkasa harkokin kasuwanci, da zai baiwa 'yan kasuwa damar mallakar asusun banki na kamfanoninsu, da kuma samun bashi da sauran tallafi daga gwamnati," a cewar sanarwar da hukumar ta fitar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng