Abin da Ya Sa Likitoci Ba Sa Zama a Asabitocin Jihar Kogi, CMD Ya Yi Karin Bayani

Abin da Ya Sa Likitoci Ba Sa Zama a Asabitocin Jihar Kogi, CMD Ya Yi Karin Bayani

  • Hukumar gudanarwar asibitin kwararru na jihar Kogi ta sanar da cewa har yanzu likitoci ba sa neman aiki a asibitin duk da bude kofar da suka yi
  • A cewar Dr. Ish Adagiri, hukumar asibitin ta samu izinin daukar sabbin likitoci tun lokacin Yahaya Bello, amma har yanzu ba wanda ya nema
  • Adigiri ya koka kan yadda likitoci ke ajiye ayyukansu a Najeriya suna tsallakewa zuwa kasashen ketare don yin aiki da zummar tara makudan kudade

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kogi - Isah Adagiri, babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin kwararru a jihar Kogi, ya ce sabbin likitoci na da wuyar samu a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Adagiri ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi kan kasafin kudin shekarar 2024 a majalisar dokokin jihar Kogi da ke Lokoja, babban birnin jihar.

Likitoci ba sa neman aiki a asibitin Kogi
Asibitin kwararru na jihar Kogi ya ce sabbin likitoci na da wuyar samu a 'yan kwanakin nan. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Ya ce duk da cewa Yahaya Bello ya amince wa mahukuntan babban asibitin maye gurbin duk wani likitan da ya bar aiki, amma hakan ya ci tura, saboda likitoci sun ki neman aiki a asibitin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likitoci sun kaurace wa asibitin KSSH - CMD Adagiri

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito shi yana cewa:

"Likitoci da yawa sun yi kaura zuwa wasu jihohin ko kasashen waje, kuma duk kokarinmu na maye gurbinsu da wasu ya ci tura, mun gaza samun likitocin da za mu yi aiki da su."
"Ba bakon labari ba ne yadda likitocin Najeriya ke fita zuwa kasashen waje neman manyan ayyuka, lamarin da ya tabarbarar da ayyukan lafiya a asibitin mu.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya dakatar da masu gadin asibiti kan aikata laifi 1 tak

Shugaban asibitin ya kara da cewa:

"Akwai matsaloli da yawa da ka iya samun likitocin da ke fita kasashen waje neman abin duniya, za ka taras suna yin abubuwa masu yawa don ganin sun samun kudi."

Dr. Adagiri ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara albashi da alawus ga ma'aikatan lafiya a kasar, hakan zai rage yawan likitocin da ke fita kasar waje neman aiki, rahoton The Cable

Ana damfarar 'yan Najeriya da sunan sama masu aiki a kasashen waje - MDD

A wani labarin, Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi 'yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan yayin da suke fafutukar neman ayyukan yi a kasashen waje.

Shugaban hukumar IOM na majalisar ya ce yanzu haka akwai sama da 'yan Najeriya 1,000 da aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel