Babban Fasto Ya Ki Amincewa da Nadin da Gwamna Oborevwori Ya Yi Masa, Ya Ce “Hakan Raini Ne”

Babban Fasto Ya Ki Amincewa da Nadin da Gwamna Oborevwori Ya Yi Masa, Ya Ce “Hakan Raini Ne”

  • Babban malamin addinin Kirista a jihar Delta, ya yi watsi da wani nadin mukami da gwamnan jihar Oborevwori ya yi masa
  • Archbishop Iboyi Godday wanda ya bayyana nadin matsayin "cin fuska" ya ce gwamnan ya yi nadin ba tare da neman izininsa ba
  • A wata sanarwa, Oborevwori ya nada Arcbishop Iboyi da wasu mutum hudu matsayin mambobin hukumar alhazan Kirista ta jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Delta - Wanda ya kafa cocin Overflow Chapel da ke Sapele a jihar Delta, Archbishop Iboyi Godday, ya ki amincewa da nadin da Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi masa a matsayin mamba a hukumar alhazai da walwala ta Kirista.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya aike da muhimmin gargadi ga Gwamna Fubara

Wata sanarwa ta ce Gwamna Oborevwori, ya amince da nadin Arcbishop Iboyi da wasu mutum hudu matsayin mambobin hukumar, yayin da Apostle Sylvanus Okorote ya zama shugaba.

Fasto ya ki karbar mukamin da gwamnatin Delta ta yi masa
Archbishop Iboyi Godday ya ki karbar tayin mukamin mamba a hukumar alhazan Kirista ta jihar Delta. Hoto: @RtHonSheriff, @PkmOverflowChapel
Asali: Facebook

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar jiya, shugaban cocin masarautar Okpe, ya bayyana cewa an yi nadin ne ba tare da amincewar sa ba, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Archbishop Godday ke kallo game da nadin

Yayin da ya bayyana nadin a matsayin cin fuska, Arcbishop Iboyi ya ce ba shi da sha’awar zama mamba a hukumar, don haka ya ki amincewa da nadin.

Tribuneonline ta ruwaito sanarwar malamin addinin na cewa:

"An ja hankalina ga wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa an nada ni mamba a hukumar alhazai ta kirista ta jihar Delta ba tare da izinina ba.

Kara karanta wannan

An sake shigar da fitaccen jarumin fina-finai dakin tiyata don gutsere masa kafa, ba ya iya magana

"Ina amfani da wannan kafar don sanar da duk wanda ya yi mun wannan cin fuskar da sunan nadi cewa ba ni da sha'awar mukamin kuma na yi watsi da shi."

Kasafin 2024: Wike ya roki majalisa ta amince ma'aikatarsa ta samu N17bn

A wani labarin, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya roki kwamitin ma'aikatar FCT ya amince da naira biliyan 17 da aka warewa ma'aikatar a kasafin 2024.

Nyesom Wike, ya zayyana wasu manyan ayyuka biyar da ma'aikatar za ta yi a shekarar 2024 idan har ta samu wadannan kudade, Legit Hausa ta ruwaito.

Jim kadan bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa zauren majalisar dokokin tarayya da kasafin 2024, ministoci suka fara kare kasafin da aka ware wa ma'aikatarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel