NNPP da Jam’iyyun Adawa 7 Sun Hada Kai a Shirin Kifar da APC Daga Mulki a 2027

NNPP da Jam’iyyun Adawa 7 Sun Hada Kai a Shirin Kifar da APC Daga Mulki a 2027

  • Jam'iyyun adawa a fadin Najeriya sun fara hadaka kan yunkurin kayar da jam'iyyar APC mai mulki a babban zaben 2027
  • Jagororin hamayya da dama ne suka halarci taro na musamman a jihar Kaduna domin tattaunawa kan yadda za su karbi mulki
  • Shugaban taron, Lawal Nalado ya bayyana irin matakan da za su dauka wajen ganin sun samu nasara wurin kawar da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gamayyar jam'iyyun adawa sun fara yunkurin samar da hadaka kan kawar da jam'iyyar APC a babban zaben 2027.

Jam'iyyun adawa
Jam'iyyun adawa sun fara shirin kwace mulki daga APC a 2027. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Jam'iyyun adawa suna harin wurin APC

Hakan ya biyo wani taro na musamman na neman hadaka da jam'iyyar adawa ta ADC ta jagoranta a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sama da 40 sun mika wuya a jihar Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da Daily Trust ta wallafa a ranar Juma'a ya tabbatar da cewa jam'iyyu takwas ne suka halarci taron.

Me aka tattauna a taron 'yan adawan?

Rahotanni da suka fito bayan taron sun nuna cewa jam'iyyun sun hadu ne domin ganin yadda za su samu karfin tunkarar jam'iyya mai mulki a zaben 2027.

Jam'iyyun sun kara da cewa zaman nasu ya mayar da hankali kan yadda za a ceto al'ummar Najeriya daga cikin halin da suke a yanzu, cewar jaridar Punch.

Jam'iyyun da suka halarci taron adawan

Daga cikin jam'iyyun da suka halarci taron sun hada da jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano. Sauran jam'iyyun sun hada da PRP, AFGA, SDP, IPAC da kuma CUPP.

Sun ce akwai bukata ta musamman wurin tabbatar da samun hadin kan yan kasa domin cimma nasara a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kama rijiyoyin mai na bogi a jihar Ribas

'Yan adawa sun ce APC ta gaza

Shugaban taron, Lawal Nalado ya ce akwai bukatar gaggawa wajen magance matsalolin da 'yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Nalado ya kuma kara da cewa lallai gwamnatin APC ta gaza daukan matakin da ya dace kan magance matsalolin Najeriya.

Shugabannin sauran jam'iyyun sun bayyana muhimmancin wayar da kan masu zabe a cikin tafiyar da suka dauko.

Pat Utomi ya koka kan halin 'yan siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake shirye-shiryen haɗaka na jam'iyyun adawa, daya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa ya magantu kan lamarin.

Farfesa Pat Utomi wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben baya ya ce a yanzu ƴan siyasa kawai suna yin mulki domin kansu ne ba wai yan kasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel