Dakarun Sojin Najeriya Sun Ƙara Samun Babbar Nasara Kan Yan Bindiga a Jihar Sakkwato

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ƙara Samun Babbar Nasara Kan Yan Bindiga a Jihar Sakkwato

  • Dakarun sojojin Operation Hadarin Daji sun sake samun babbar nasara kan yan ta'adda da suka hana jama'a zaman lafiya a Sokoto
  • A wani samame da suka kai cikin daji jiya Alhamis, sojojin sun halaka ƴan bindiga uku kuma sun ceto mutum shida
  • Bayan haka kuma sun kwato makamai da babura, sun tarwatsa dukkan sansanonin da suka gano a jejin

Jihar Sokoto - Dakarun sojin rundunar Operation Hadarin daji sun samu nasarar murƙushe yan bindiga uku har lahira a jihar Sakkwato.

Hukumar sojin ƙasan Najeriya ce ta tabbatar da samun wannan nasara a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Sojoji sun samu nasara a jihar Sakkwato.
Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga Ukua, Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Sokoto Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sanarwan ta bayyana cewa a ci gaba da ƙoƙarin kakkabe ƴan ta'adda a shiyyar Arewa maso Yamma, dakarun sojin sun matsa kaimi wajen kai samame maɓoyar yan bindiga.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2

Rundunar sojin ta ce jami'an sun kai samame wani daji a ƙauyen Bauni da ke jihar Sakkwato, inda suka kashe yan bindiga uku suka kwato makamai da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar hukumar sojin, yayin da samamen da sojoji suka kai dajin ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, 2023, "sun yi musayar wuta da ƴan ta'adda na tsawon sa'o'i."

Sai dai ta bayyana cewa ƙarfin kayan aikin sojoji da jajircewarsu a fagen daga ya sa suka ci ƙarfin gungun ƴan ta'addan, wanda ya tilasta masu tserewa daga mafakarsu.

Dakarun soji sun ceto mutum 6 da aka sace

Bisa wannan nasara, sojoji sun ceto mutane shida da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su, "Yayin da kuma suka halaka yan bindiga uku, suka kwato bindiga kirar AK47 guda biyu da alburusai."

"Dukkan sansanonin ƴan bindigan da aka gano da baburan da aka kwato sojojin sun ƙone su nan take ba tare da ɓata lokaci ba," in ji sanarwan.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji yan ta’adda a Kaduna, sun kwato makamai da babura

Yan bindiga sun bakunci lahira a jihohi biyu

A wani rahoton kun ji cewa Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar tarwatsa mafakar ƙasurguman 'yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto.

Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga biyar, sun kwato makami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel