“Zai Hadiye Cokali”: Bidiyon Wani Dan Najeriya a Gidan Abinci Ya Girgiza Intanet

“Zai Hadiye Cokali”: Bidiyon Wani Dan Najeriya a Gidan Abinci Ya Girgiza Intanet

  • Wani bidiyo da ke nuno wani mutum yana sharholiya da askirin da kayan makulashe a wani gidan cin abinci ya yadu a soshiyal midiya
  • Bidiyon ya nuno mutumin yana cin abincinsa hankali kwance ba tare da ya damu da ko akwai wani a wajen ba
  • Mutane da suka kalli bidiyon wanda aka wallafa a TikTok sun yi martani masu ban dariya kan yanayin mutumin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo mai ban dariya na wani dan Najeriya a gidan cin abinci ya bar mutane cikin mamaki a TikTok.

Bidiyon ya nuno matashin yana shan askirin da cincin a wani wajen cin abinci inda ya mayar da hankalinsa kacokan a kansu.

Kara karanta wannan

Yadda mutumin da ke aikin wanke bandaki a turai ya siya gida daga albashinsa, bidiyon ya yadu

Matashi yana sharholiya a gidan abinci
“Zai Hadiye Cokali”: Bidiyon Wani Dan Najeriya a Gidan Abinci Ya Girgiza Intanet Hoto: @idaks_/TikTok.
Asali: TikTok

An hasko wani mutum yana hadiyar abincinsa a wajen cin abinci

Bidiyon wanda @idaks__ ya yada ya hasko mutumin cikin kwanciyar hankali yana tauna abincinsa, yana mai nuni kamar gaba daya rayuwarsa ta dogara a kansa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farin cikinsa ya dauki hankalin masu kallo, wanda hakan ya sa bidiyon ya yadu a fadin kafafen soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon matashi da ke kwasar girki

Bidiyon ya haddasa dariya da ban mamaki daga wajen mutanen da suka ci karo da shi.

@Big_Kamal ya yi martani:

"Wwan ya sha wahala a rayuwa."

@val ya ce:

"Askirin da cicin duniya ne."

@aniyaaa ya ce:

"Yallabai ya ga abubuwa a rayuwar nan. Wani ya rike shi fa."

@Emmadoski_Ad ya yi martani:

"Mutumin nan ba shi da budurwa shine dalilin da yasa yake farin ciki da jin dadi a rayuwar nan."

Kara karanta wannan

"Dan nan zai haddasa rigima": Bidiyon kyakkyawan yaro mai kama da mace ya tsuma zukatan jama'a

@oby ya yi martani:

"Akwai wata yarinya da ta ci masa kudi! yanzu ya waye yayana na unguwa."

@jerseyy ya yi martani:

"Sai kuma sai hada da cokalin."

Budurwa ta koka kan yaudarar saurayi

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka yayin da ta sanar da cewar saurayinta na shekaru uku ya auri wata daban a kwanan nan.

Matashiyar mai suna @sexysica_, ta magantu kan soyayyarsu a TikTok yayin da ta dungi zubar da hawaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel