Yadda Yaran Turawa da Mahaifinsu Suka Sharbi Kuka a Filin Jirgi Kan Rabuwa Da Mai Aikinsu
- Wani bidiyo mai tsuma na bature da yaransa suna sharban kuka a filin jirgin sama yayin da mai aikinsu ta koma kasarta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
- Yayin da baturen ya yi wa mai aikin tasa rakiya, yaran sun gaza yin bakwana da ita cikin sauki inda suka dunga bin ta da gudu
- Mai aikin wacce ta tsaya sannan ta dauki lokaci tana rungumar yaran da suka gaza barinta cikin hawaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani bidiyo da ya yadu da yaran turawa suna sharban kuka a filin jirgin sama yayin da mai aikinsu zata tafi ya tsuma zukata a soshiyal midiya.
Mai aikin wacce ta kasance bakar fata da aka ambata da suna Rosie, ta rigada ta yi nisa lokacin da yaran wanda ya dauketa aiki suna ruga wajenta, inda suka ki bari ta tafi.
Baturen da matarsa sun yi kokarin janye yaransu domin ba Rosie damar tafiya amma sai suka nuna turjiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon da aka gano a TikTok, an nuno yadda mai aikin ta rungume yaran sannan ita ma ta fashe da kuka yayin da take kallonsu suna zub da hawaye.
Baturen ma ya sharbi kuka
Ta kai inda aka gano shi kansa baturen yana kokarin boye hawayen da ke kwaranyowa daga idanunsa.
A wani bidiyo daga lamarin, mutumin ya bukaceta da ta dawo, cewa ba za su iya rayuwa babu ita ba.
Kalli bidiyon a kasa:
Bidiyon ya tsuma zukata
melaniethaker752 ta ce:
"Hatta mahaifin ma kuka yake yi Rose ki ji dadin hutunki."
Mayralucky7:
"Wayyo Allah! Wannan ya karya mani zuciya an hada yara da mutum na musamman kamar Rosie wacce ke sonsu, kuma tana kula da su da zuciya daya❤️Allah ya yi mata albarka."
oliviachi2222:
"Allah ya yi wa Rosie tamu albarka, wata irin mace mai ban mamaki da fatan yarana za su ajiye zuciyarsu mai tsarki, Allah ya yi masu albarka."
Charmayne Harrell:
"Me ya sa ni kuka tare da yaran Rosie. Daya daga cikinsu ta kirata da mama."
Longorrrriiia:
"Me yasa na ji ina son Rosie da alama tana da dadin zama."
Budurwa ta wawure kudin amarya da ango
A wani labari na daban, wani bidiyo da ke yawo ya hasko wata matashiyar budurwa da aka dauka tana wawure kudin liki da ya kamata ace tana taya amarya da ango kwashewa.
Wani dan TikTok, @preshkc1, wanda ya yada bidiyon a dandalin soshiyal midiya ya ce:
"Wannan ne dalilin da yasa nake sa hannuna na kwashe kudina."
Asali: Legit.ng