‘Haka Dama Najeriya Take’: Daga Dura Najeriya, Yaro Ya Firgita, Ya Shiga Mamaki

‘Haka Dama Najeriya Take’: Daga Dura Najeriya, Yaro Ya Firgita, Ya Shiga Mamaki

  • Wata mata ta nadi bidiyon yadda danta ya yi na ban dariya da ya ga dandazon jama'a a filin jirgin saman Najeriya a ziyararsa ta farko
  • Da yake bayyana rudani da firgici, ya yiwa mahaifiyarsa wata tambaya da ta baiwa ‘yan Najeriya da dama dariya
  • Jama’a da dama sun ga abin da ya faru, sun kuma bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wani karamin yaro ya kasa gaskata idanuwansa yayin da ya ga tulin mutane da yawa a filin jirgin saman Najeriya bayan ya isa kasar a ziyararsa ta farko.

Mahaifiyarsa ta bayyana cewa ziyararsa ta farko Najeriya kenan, inda ya kwashe da dariya har ya rude da ganin jama'a a filin jirgin.

Ta nadi abin da ya faru mai ban dariya yayin da suke tattaunawa. Cikin rudani a fuskarsa yaron ya kada baki yace, dama haka Najeriya take.

Kara karanta wannan

"Nuna mun alama": Budurwa ta ziyarci kabarin mahaifinta, ta nemi ya girgiza bishiya, bidiyon ya yadu

Yaro ya tsorata da shigowa Najeriya
Daga shiga Najeriya yaro ya firgita | Hoto: Maskot, Stringer
Asali: Getty Images

Matar dai ta bayyana mamakin yadda yaron ya ji, kana ta tsaya tunanin ya dan nata ke son ganin Najeriya idan ba haka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon da aka yada a kafar TikTok ta hannun @stoner_012 ya jawo cece-kuce da yawa, ya kuma sa mutane suna ta magana.

Wasu kuwa, sun bayyana kadan daga abubuwan da zai ci karo dasu a matsayinsa na mai ziyara a kasa irin Najeriya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@MummyJael :

"Ya kadu kuma abin da zai faru da 'ya'yana kenan saboda suna da buri da yawa! Kada dai a fada musu."

Daniel:

"Abin babu kyau dan yaro, kada ka damu za a fada ma Tinubu ya amince da ba da kyautar Kirsimeti."

ANUOLUWAPO OLUTOLA:

"Ku fada masa haka siddan ake dauke wuta ana kawowa. Kada ya fara kuka."

Kara karanta wannan

Matashi ya nuna yadda wayar iPhone dinsa ta makale a tukunya bayan ya yi kuskure wajen girki

yes_I'm_naveen:

"Watakila ya yi zaton mutane na rayuwa a cikin daji da bishiyoyi ne a Najeriya."

MBen:

"Shin babu mutane ne a jirgin da ya hau ya zo? Me yasa mutane za su bashi tsoro?"

Cynthia:

"A filin jirgnin sanda kake kuma har ka fara korafi ka bari ka shigo titi mana."

Budurwa ziyarci kabarin mahaifita

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta tsuma zukata a TikTok bayan ta yada wani bidiyo na ziyarar da ta kai kabarin mahaifinta.

Matashiyar mai suna @Iromicc a TikTok ta isa kabarin mahaifinta da ya rasu don yin magana da shi amma bata ji amsa daga gare shi ba.

A cikin bidiyo da ya yadu, ta roke shi da ya girgiza bishiya ko wani abu domin ta tabbatar da cewar yana sauraronta, amma babu abun da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel