Yadda Mutum-Mutumi Mai Kama da Mace Ke Aikin Bada Abinci a Gidan Abinci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yadda Mutum-Mutumi Mai Kama da Mace Ke Aikin Bada Abinci a Gidan Abinci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • An gano wata mutum-mutumi wacce ke aikin bada abinciki a gidan cin abinci tana aikinta a yanayin da ya sa mutane dariya
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutum-mutumin ka kawo kwanon abinci sannan ta daura shi a kan tebur
  • Tana ta abun sai kace wani na amfani da na'urar rimot wajen bata umurni kan abun da za ta yi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

An gano wata mutum-mutumi mai hikima wacce ke aiki a matsayin mai kula da kwastamomi a wani gidan cin abinci.

A wani bidiyo da ya yadu wanda @user8618773353018 ya wallafa, mutum-mutumin ta yi shiga kamar wata mace sanye da riga da wando harda takalmi.

Kara karanta wannan

Ko awanni 10 ba a yi ba da mutuwar mahaifinsu, an gano iyali suna cin abinci hankali kwance

Mutum-mutumi mai kama da mace na bada abinci
Yadda Mutum-Mutumi Mai Kama da Mace Ke Bada Abinci a Gidan Cin Abinci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: TikTok/@user8618773353018.
Asali: TikTok

Tana ta tafiya a hankali zuwa cikin gidan cin abincin dauke da dan karamin kwano da abinci a hannunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hankali ta duka sannan ta ajiye kwanon abincin a kan teburin da ke gabanta. Sai dai kuma, tana ta yi kamar mai karbar umurni daga wajen wani.

Bidiyon ya haifar da martani daban-daban daga jama'a bayan an wallafa shi a TikTok yayin da mutane suka garzaya sashin sharhi domin kimanta aikin mutum-mutumin mai aikin bada abinci.

Sai dai kuma, saboda yanayin yadda take abu, wasu sun yi tunanin cewa mutum ce da gaske take kwaikwayon mutum-mutumi.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da mutum-mutumi ke aikin bada abinci a gidan cin abinci

@essay ya ce:

"Tana bayar da....kazar roba."

@BEBAN ta ce:

"Zan iya yarda mutum-mutumi ce kuwa?"

@pisey ta yi martani:

Kara karanta wannan

Kano: Kwamishinan 'yan sanda ya dauki mataki kan sifetan da ya yi ajalin matashi yayin zanga-zanga

"Mutane ko mutum-mutumi."

@Rebeca Ramírez ta ce:

"Yarinyar gaske ce. Ba mutum-mutumi bace."

@Nassy ta ce:

"Shakka babu, ba mutum-mutumi bace."

@Nunzia ta ce:

"Ba mutum mutumi bace. Yarinya ce wacce ke kwaikwayon mutum-mutumi da kyau."

@Doreen ta ce:

"Shin ni kadai ce wacce za ta tsorata da mutum-mutumi irin wannan?"

Iyalin da suka rasa mahaifi sun bada mamaki

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani rubutu da ya yi fice a Twitter, wani dan Najeriya ya tuna wani abun ban mamaki da ya gani wani lokaci da ya gabata.

Mutumin mai suna @FotoNugget a Twitter ya ba da labarin yadda abokan arziki suka ziyarci wasu iyali da sassafe bayan mahaifinsu ya rasu cikin dare.

Ga mamakinsu, sun gano yara da matar mutumin suna cin abinci safe hankali kwance, ga dukkan alamu abun bakin cikin da ya riske su bai dame su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng