Ko Awanni 10 Ba a Yi Ba da Mutuwar Mahaifinsu, An Gano Iyali Suna Cin Abinci Hankali Kwance

Ko Awanni 10 Ba a Yi Ba da Mutuwar Mahaifinsu, An Gano Iyali Suna Cin Abinci Hankali Kwance

  • Wani dan Najeriya ya haddasa cece-kuce bayan ya ba da labarin wasu iyali da suka rasa mahaifinsu cikin dare
  • Sai dai kuma, bayan abun bakin cikin da ya same su na mutuwar mahaifinsu, an gano iyalin suna cin abincin safe hankali kwance washegari
  • Labarin ya yi fice yayin da mutane suka bayyana halin da suka tsinci kansu yayin da suke alhinin rashin masoyansu ta hanyoyi mabanbanta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani rubutu da ya yi fice a Twitter, wani dan Najeriya ya tuna wani abun ban mamaki da ya gani wani lokaci da ya gabata.

Mutumin mai suna @FotoNugget a Twitter ya ba da labarin yadda abokan arziki suka ziyarci wasu iyali da sassafe bayan mahaifinsu ya rasu cikin dare.

Kara karanta wannan

Basaraken Abuja zai biya naira miliyan 2 kudin fansar matarsa da aka yi garkuwa da ita

Iyalin sun ci abinci hankali kwance bayan mutuwar mahaifinsu
An yi misali da hoton ne, mutanen jiki basu da alaka da labarin Hoto: Lawrence Manning, TONY KARUMBA/ Getty Images.
Asali: Getty Images

An gano iyali suna cin abincin safe hankali kwance bayan mutuwar mahaifinsu

Ga mamakinsu, sun gano yara da matar mutumin suna cin abinci safe hankali kwance, ga dukkan alamu abun bakin cikin da ya riske su bai dame su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Mahaifin mutum ya rasu da daddare, an je gaishe su washegari da safe-sun tarar da yara da matar suna cin abinci. Ko awanni 10 ba a yi ba da mutuwarsa."

A rubutun nasa, ya nanata dan takaitancen lokaci a tsakani iyalin sun koma harkokinsu na yau da kullun bayan mutuwar mahaifinsu.

Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda mutane ke juyayi ta hanyoyi daban-daban

Nan take jama'a suka taru a sashin sharhi domin bayyana ra'ayoyinsu da yanayin yadda kowa ke alhininsa.

Mutane da dama sun jaddada cewar mutane na da hanyoyin nuna alhininsu daban-daban kuma babu wata hanya guda da za a ce ita ce ta dace da alhinin wanda aka rasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani matashi ya tarwatsa bikin auren tsohuwar budurwarsa ya girgiza intanet

@Progressiv ya ce:

"A duk yanayin da kake ciki a rayuwa ka yi kokari ka ci abinci."

@rich ya yi martani:

"Ba za ka fahimci alhinin rashi ba sai kana cikinsa. Namu ba abinci bane zamani ne da za ka iya aron fina-finai. Mun ari fina-finai da dama a kullun. Duk wanda ya gan mu zai yi zaton mun manta ne amma bamu manta ba kuma har lokacin bamu manta ba."

@Aniss deremi ta ce:

"Suna bukatar cin abinci sosai don samun karfin yin kuka mana."

@Hare ta yi martani:

"Sun san baba baya nan kuma kuka ba zai dawo da shi ba. Addu'a ita baba ke bukata."

@kendra_m ya ce:

"Bana tunanin wannan sabon abu ne saboda ina ganin abubuwa daban-daban a kullun."

Matashi ya fadi sirrin aikinsa a Turai

A wnai labarin, mun ji cewa wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya yana samun albashi N204k duk kwanan duniya a matsayin ma'aikacin agaji.

Mutumin ya wallafa wani bidiyo a TikTok don bayar da labarinsa amma ya ce aikin sam babu sauki saboda yana kula da wani tsoho ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng