"Babu Wanda Ya Tsira": Mutum-Mutumi Ya Samu Tangarda, Ya Kashe Ma'aikaci Kafin a Farga
- A wani mummunan al'amari da ya afku, mutum-mutumi ya kashe wani mutum a wata masana'antar sarrafa barkono a Koriya ta Kudu
- Mutumin na kula da ayyukan na'urar mutum-mutumin ne kafin gwaji kwatsam sai al'amarin ya afku
- Wannan ba shine karo na farko da mutum-mutumi ke ji wa mutum ciwo ko yin kisa ba a Koriya ta kudu yayin da kwararru da dama suka yi korafi
Mutum-mutumi ya kashe wani mutum a ata masana'antar sarrafa barkono a Koriya ta Kudu bayan ya yi kuskuren daukar shi a matsayin kwalin kayan lambu, kamar yadda BBC ta rahoto.
Wanda abun ya ritsa da shi, ma'aikacin kamfanin dillancin mutum-mutumi wanda ke ganiyar shekaru 40, yana cikin kula da ayyukan na'urar mutum-mutumin a daren ranar Laraba, lokacin da na'urar ta kama shi tare da rusa masa fuska da kirji.
An kwashe shi zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa
An kera mutum-mutumin ne don daukar kwalayen barkono da tura su zuwa inda za a nika su. Mutumin na ta duba na'urar gabannin gwajin da za a yi a ranar Juma'a, amma sai mutum-mutumin ya samu matsala sannan ya gaza banbance shi da kwalayuen, kamfanin ya rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya afku ne a rukunin gonaki na Donggoseong Export da ke lardin Gyeongsang ta Kudu, wanda yake mallaki masana'antar.
Wani jami'in kamfanin ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin sannan ya yi kira da a samar da tsarin daidaitawa da bayar da kariya.
Mutum-mutumi ya saba barna a Koriya ta kudu
Wannan ba shine karo na farko da mutum-mutumi ke raunata mutum ko aikata kisa ba a Koriya ta kudu.
A watan Maris, wani mutum mai shekaru 50 ya samu munanan rauni bayan da wani mutum-mutumi ya murkushe shi lokacin da yake aiki a wata masana'antar kera kayayyakin mota.
Wasu masana sun yi gargadin kan illar da ke tattare da na’urar mutum-mutumi a yayin da suke samun ci gaba da cin gashin kansu.
A shekarar 2017, gungun masu bincike na sirri da masu ilimin dabi'a sun fitar da wata budaddiyar wasika inda suka yi kira da a hana amfani da makamai masu cin gashin kansu, ko "mutum-mutumi masu kisa", wadanda za su iya kai hari ba tare da sa hannun dan Adam ba.
Sun bayyana cewa irin wadannan makamai za su zama barazana ga tsaro da kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, kuma za su iya haifar da wata sabuwar nau'in makamai.
Mutum-mutumi na ba da hannu a Abuja
A wani labari, mun ji cewa an gano wani mutum-mutumi yana ba da hannu a wani titin Abuja mai cike da cunkoson ababen hawa.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, an gano mutum-mutumin da ke tsaya a tashar yan sanda kan hanyar inda yake ba ababen hawa hannu.
Asali: Legit.ng