Gwamna Ya Tona Gaskiyar Halin da Buhari Ya Damkawa Tinubu Tattalin Arzikin Najeriya

Gwamna Ya Tona Gaskiyar Halin da Buhari Ya Damkawa Tinubu Tattalin Arzikin Najeriya

  • Gwamnan jihar Anambra ya yi bayanin halin da Bola Tinubu ya tsinci tattalin arzikin Najeriya da ya hau kan mulki
  • Charles Chukwuma Soludo yana da ra’ayin cewa sabon shugaban ya gaji mushen doki ne da aka dauka yana da lafiya
  • Abin da ya jawo tashin Dala a kan Naira kamar yadda Farfesa Soludo ya fada shi ne yadda bankin CBN ya rika bada bashi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaji mataccen tattalin arziki ne.

Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan bayani ne lokacin da aka yi hira da shi a shirin siyasa na tashar Channels a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Mataimakin Sanusi a bankin CBN ya fito ya soki hukuncin zaben gwamnan jihar Kano

Charles Soludo ya yi karin haske a game da yadda Dalar Amurka ta ke tashi a kan Naira.

Chukwuma Charles Soludo
Soludo ya ce Buhari ya kashe tattalin arziki Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kuskuren bankin CBN a lokacin Buhari"

Daga cikin abubuwan da su ka jawo matsalar da ake fuskanta a yau, Gwamnan ya ce bankin CBN ya rika buga kudi a baya ba a kan ka’ida ba.

A lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki, ana zargin Godwin Emefiele ya saba dokar 2007, inda ya amince aka yi buga kudi ta bayan fage.

Jawabin tsohon Gwamnan naCBN

"Dole mu duba inda mu ka fito. Mun zauna a kasar nan mu na ganin hukumomi suna buga kudi ta hanyar da ba ta halatta ba.
Saboda a magance matsalar da mu ke shiga yau, shiyasa muka kawo doka da za ta hana CBN ba gwamnati bashi da ganganci."

- Gwamna Charles Chukwuma Soludo

Kara karanta wannan

Bayan zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fadi burin da ya rage masa a Duniya

Ina Buhari da Emefiele su ka kai dokar CBN?

Daily Trust ta rahoto Farfesa Soludo ya na cewa dokar da aka kawo ta hana CBN ba gwamnati aron abin da ya zarce 5% na kudin shigar bara.

Ko da gwamnatin tarayya ta karbi aron wannan kudi daga hannun CBN, zuwa karshen shekara ya zama dole a biya bashin a cewar Soludo.

"Tinubu ya gaji mushen doki daga Buhari"

Masanin tattalin arzikin ya ce ana gani CBN ya rika buga N4tr, N10tr da N15tr a kasar, ra'ayin ya zo daidai da na magajinsa, Muhammadu Sanusi.

Saboda haka Soludo ya sake nanata cewa gwamnai mai-ci ta gaji tattalin arziki ne na mushe doki wanda yake tsaya, duk an dauka yana da rai.

Dazu aka ji labari wasu Yarbawan Kano sun ce mutane za su iya kai masu hari saboda tsige Abba Kabir Yusuf da aka yi a kotun daukaka kara.

Kungiyar Yarbawan ta roki Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II da Olusegun Obasanjo su zauna da Bola Tinubu saboda gudun rigima ta kaure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel