WAEC Ta Rike Sakamakon Wasu Dalibai Bayan Gano Sun Yi Amfani da AI Wajen Amsa Tambayoyi

WAEC Ta Rike Sakamakon Wasu Dalibai Bayan Gano Sun Yi Amfani da AI Wajen Amsa Tambayoyi

  • An rike sakamakon jarabawar WAEC na dalibai daga makarantu 235 saboda amfani da amsoshin da suka samu ta hanyar fasahar AI a lokacin jarrabawarsu a Ghana
  • Kakakin hukumar ta WAEC a Ghana, John Kapi, ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan tangardar a jarrabawar
  • Kapi ya bayyana cewa WAEC za ta gayyaci duk wadanda abin ya shafa ta hanyar sakon SMS ko buga sunayensu a jaridu domin kare kansu

Ghana - Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) a Ghana ta hana sakin sakamakon jarrabawar dalibai daga makarantu 235 saboda amfani da amsoshin da suka samu ta hanyar fasahar 'komai na iya' ta AI.

Kakakin hukumar ta WAEC a Ghana, John Kapi, wanda ya bayyana hakan ya ce amfani da AI na daya daga cikin kura-kurai da hukumar jarabawar ta gano a yayin makin takardun daliban da suka zana jarrabawar a watan Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Abba Gida-Gida ya samu matsala, aka yi laifi wajen Rusau a Jihar Kano

WAEC ta rike sakamakon jarrabawar daliban Ghana
WAEC ta rike sakamakon jarrabawa a kasar Ghana | Hoto: @olatunji_Godson
Asali: Twitter

Kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito, Kapi ya bayyana a yayin wata hira da cewa tabbas daliban sun yi amfani da AI wajen ba da amsoshin tambayoyin da aka yi musu.

Abin da ya faru a WAEC

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wasu daliban sun rubuta cewa ba su da masaniya kan kalmomin da aka yi amfani da su a cikin takardun amsar. Yayin da wasu suka ce "Ba za su iya gano abin da aka yi amfani da shi a cikin takardun ba."

Ya ce hakan ya nuna cewa daliban sun nemo amashoshin ne da wayoyinsu na hannu a cikin dakunan rubuta jarrabawa.

Kakakin hukumar ta WAEC ya ce an samu irin wannan shirmen ne a cikin amsoshin da wasu daliban suka bayar, CitiNewsRoom ta tattaro.

Mafitar da WAEC ta samo

Kapi ya ce wannan ne karo na farko da WAEC ta gano irin wannan rashin kitimurmura ta saba ka’ida a jarabawar.

Kara karanta wannan

PDP ta nemi EFCC ta ba Gwamnan Zamfara hakuri kan wallafar da ta yi a soshiyal midiya

Ya ci gaba da cewa:

"Muna son hada kai da hukumar ilimi game da tsauraran ka'idojin amfani da wayoyin hannu a bangarorin biyu."

WAEC ta kawo CBT irin na JAMB

A wani labarin, hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC), ta ce za ta fara amfani da tsarin na'ura mai kwakwalwa (CBT) wajen gudanar da jarrabawar kammala sakandare (SSCE).

Hukumar jarrabawar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, cewar za a yi watsi da tsarin zana jarabawar ta hanyar amfani da takarda da fensir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel