Shari'ar Gwamnan Kano: Jami'an Tsaro Sun Bankado Wani Shirin Tayar da Tarzoma, Sun Gargadi Al'umma

Shari'ar Gwamnan Kano: Jami'an Tsaro Sun Bankado Wani Shirin Tayar da Tarzoma, Sun Gargadi Al'umma

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi al'umar jihar Kano da su kauracewa duk wani nau'in zanga-zanga ko taron jama'a da ka iya hadda fitina a jihar
  • Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri da ke nuni da cewa mambobin wata jam'iyya na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan da Kotun Daukaka Kara ta kori Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano a ranar Juma'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi duk wasu magoya bayan wata jam’iyya da ke shirin gudanar da zanga-zanga a jihar biyo bayan hukuncin da kotun Daukaka Kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Shari’ar gwamnan Kano: Yan APC sun fara azumin neman nasara yayin da Abba ya garzaya Kotun Koli

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel wanda ya yi wannan gargadin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Rundunar 'yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta gargadi masu shirin tada tarzoma a Kano biyo bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara na korar Abba daga gwamnan Kano Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Kwamishinan ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar za a kama shi kuma zai fuskanci fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muna sane da masu shirin gudanar da zanga-zanga a Kano - 'Yan sanda

Ya ce akwai sahihan bayanai da rundunar ‘yan sandan ta samu cewa wasu kungiyoyin magoya bayan wata jam’iyyar siyasa na tara mutane don gudanar da zanga-zanga a titunan jihar Kano.

A cewarsa, za su gudanar da zanga-zangar ne don nuna rashin amincewarsu da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba, rahoton Premium Time.

“Bayanan sun nuna cewa masu zanga-zangar sun yi niyyar mamaye jihar ne a wani mataki da ka iya haifar da tashin hankali."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dauki mataki a wasu wurare a Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Gwamna Abba

“A kan haka, rundunar ‘yan sandan ke yin gargadi ga mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan domin duk wanda ya yi niyyar gudanar da wata zanga-zanga to ya yi hakan bisa tanadin doka."

A cewar shugaban 'yan sandan.

Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga daukacin mazauna jihar da su kwantar da hankulansu tare da kaucewa duk wani nau’i na dandazon jama'a, zanga-zanga, ko wasu ayyuka da ka iya jawo tashin hankali.

Yan APC sun fara azumin neman nasara yayin da Abba ya garzaya Kotun Koli

A wani labarin, jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi kira ga daukacin mambobinta da duk ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyin a rusau din da gwamnati ta yi a jihar da su dauki azumi a yau, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel