Kudin kasashe 20 da suka fi kowane daraja a Duniya, 5 sun sha gaban Dala da Euro

Kudin kasashe 20 da suka fi kowane daraja a Duniya, 5 sun sha gaban Dala da Euro

  • Akwai kudin kasashe biyar da su ka fi Dalar Amurka da Pound Sterling
  • Kuwaiti Dinar da Bahrain Dinar su ne kudin da su ka fi kowane daraja
  • A yau darajar Kuwaiti Dinar ta nunka na Dala fiye da sau uku a kasuwa

Mutane da-dama su na tunanin cewa Dalar Amurka ko Euro ko kuma kudin Birtaniya ne ya fi kowane daraja a fadin Duniya, amma ba haka abin yake ba.

Duk da cewa Dalar Amurka da irins Pound Sterling su na da daraja, Highest Currency ta ce akwai kudin da suka sha gabansu, daga ciki akwai Dinarin Kuwait.

Dinaran kasashen Kuwait da Bahrai sun ninka Dalar Amurka sau 3.29 da 2.65. Haka zalika akwai kudin Omani riyal da shi ma ya sha gaban Dalar ta Amurka.

Jordanian Dinar da Gibraltar Pound su ne suka cika rukunin sahun biyar na farko a wannan jeri.

A halin yanzu, Highest Currency ya nuna Pound Sterling, Euro, da Dalar Amurka sune na shida, takwas da na tara a cikin kasashen da suka fi daraja a Duniya.

Kara karanta wannan

Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure

Kuwaiti Dinar
Kudin Kuwaiti Dinar Hoto: highestcurrency.com
Asali: UGC

Wasu kudi suka fi daraja a yanzu?

1. Kuwaiti Dinar

2. Bahrain Dinar

3. Omani Riyal

4. Jordanian Dinar

5. Gibraltar Pound

6. Pound Sterling

7. Cayman Island Dollar

8. Euro

9. US Dollar

10. Swiss Franc

Swiss Franc, da Dalolin kasashen Brunei, Kanada, New Zealand, Australia da Fiji sun cira tuta. Kudin Libyan Dinar shi ne kudin da ya fi kowane daraja a Afrika.

11. Brunei Dollar

12. Canadian Dollar

13. Australian Dollar

14. Libyan Dinar

15. Singapore Dollar

16. New Zealand Dollar

17. Fijian Dollar

18. Brazilian Real

19. Israel New Shekel

20. Turkish Lira

Naira ta na kara karyewa a kasuwa

A tsakiyar makon nan ne aka ji cewa darajar Naira ta kara sukurkucewa bayan CBN ta daina ba ‘yan canji Dalar Amurka saboda zargin suna yin ta’adi.

Daga hana ‘yan kasuwa kudin kasashen waje, Dalar Amurka ta fara zabura a kasuwar canji. Rahotanni sun bayyana cewa Dala $1 ta koma Naira 505.

Asali: Legit.ng

Online view pixel