Kano: Duk da Umarnin Yan Sanda, Wasu Gungun Mutane Sun Barke da Zanga-Zanga

Kano: Duk da Umarnin Yan Sanda, Wasu Gungun Mutane Sun Barke da Zanga-Zanga

  • Masu zanga-zanga sun yi fatali da umarnin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, sun fantsama kan tituna
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Gumel ya sanar da hana duk wani nau'i na zanga-zanga a lungu da saƙo na jihar Kano
  • Jim kaɗan bayan haka ne masu zanga-zanga suka fito, kuma yanzu haka sun nufi gidan gwamnatin jihar

Kano - Wasu gungun mutane sun fara zanga-zangar lumana yanzu haka a kan titunan cikin birnin Kano duk da hukumar 'yan sanda ta haramta hakan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan rundunar yan sandan jihar Kano, Mohammed Usain Gumel, ya sanar da haramta duk wani nau'i na zanga-zanga a lungu da saƙo na jihar Kano bayan gano tuggun 'yan siyasa.

Zanga-zanga ta balle a jihar Kano.
Kano: Duk da Umarnin Yan Sanda, Wasu Gungun Mutane Sun Barke da Zanga-Zanga Hoto: Alkibla TV/Facebook
Asali: Facebook

CP Gumel ya ɗauki wannan mataki ne bayan wasu mambobin jam'iyya mai mulki NNPP da kuma jam'iyyar APC sun umarci magoya bayansu sun mamaye tituna.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Karbi Matasan da Suka Fito Zanga-Zanga a Kano, Sabbin Bayanai Sun Fito

Rahoto ya nuna 'ya'yan manyan jam'iyyun biyu na shirin gudanar da zanga-zanga ne kan zargin cin hanci da rashawa a ɓangaren shari'a na jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan 'yan sandan ya yi bayanin cewa rundunar 'yan sanda zata ɗauki duk wani yunƙuri na kauce wa haramcin zanga-zangar a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

A kalamansa, CP Gumel ya ce:

"Bisa haka ya kamata al'umma su sani cewa muna da labarin cewa APC da NNPP sun fara tara jama'a da sunan ƙungiyar ma'aikata kuma ba tare da amincewar ƙungiyar Kwadago da hukumomin tsaro ba."
“Dukkan masu shirya tuggun da na kungiyar su sani cewa duk wani yunkuri na rashin mutunta NLC da hukumomin tsaro na Kano ta hanyar yin wasa da yanayin tsaron da ake fama da shi, laifi ne da ya saɓa wa tsaron ƙasa.”

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira a Jihar Arewa

Yadda zanga-zanga ta ɓarke a Kano

Amma jim kaɗan bayan wannan umarni na rundunar 'yan sanda, masu zanga-zanga suka mamaye tituna kana suka nufi hanyar da zata kai su gidan gwamnatin Kano.

Zanga-zangar na gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugabam ƙungiyar ma'aikatan jihar Kano, (KCSF), Ibrahim Waiya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wasu mazauna Kano da suka shiga cikin masu zanga-zangar sun shaida wa Legit.ng Hausa cewa da yawan mutane ba su san da lamarin ba.

Sanusi Isiyaku, malamin wata makarantar Firamare a cikin Kano, ya ce zanga-zangar ta lumana ce ba kamar yadda rundunar 'yan sanda ke tunani ba.

Ya ce:

"Da yawan jama'a a Kano sun gudanar da harkokinsu yadda suka saba, wasu basu san ana zanga-zangar ba sai a soshiyal midiya. Duk da yan sanda sun hana, ni ina ganin ba su fahimci manufar zanga-zangar bane."
"Babu tashin hankalin da aka yi, masu zanga-zangar sun yi tattaki ne kawai zuwa gidan gwamnati, kuma gwamna ya tarbe su, sun faɗa masa dalilansu."

Kara karanta wannan

Shari'ar Zaɓen Jihar Kano: Rundunar 'Yan Sandan Ta Aike Da Muhimmin Sako Ga Masu Zanga-zanga

Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi zanga-zangar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce babban abinda suke buƙata shi ne a yi adalci a shari'ar da ke gaban Kotu.

DSS ta kama Manaja da wasu ma'aikata

A wani labarin kuma Hukumar DSS ta kama Manajan kula da zirga-zirgan jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja bayan fitar da bayanan sirri.

Jami'an DSS sun cafke Manajan tare da Manajan sashin ayyuka Victor Adamu, da wasu jami'an tashar jirgin Kaduna-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel