Zaben Gwamnan Imo 2023: ’Yan Sanda Sun Yi Arangama da Wakilan Jam’iyya, an Yi Harbe-Harbe

Zaben Gwamnan Imo 2023: ’Yan Sanda Sun Yi Arangama da Wakilan Jam’iyya, an Yi Harbe-Harbe

  • Rahotanni da ke fitowa daga jihar Imo na nuni da cewa, wasu wakilan jam'iyyar sun tare wa 'yan sanda hanya, lamarin da ya kai ga an yi harbe-harbe
  • Yan sandan sun yi kokarin yi wa jami'an hukumar zabe rakiya zuwa wata rumfar zabe tare da kayayyakin su, amma wakilan jam'iyyar su ka dakatar da su
  • A yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ke gudanar da zaben gwamna a wasu jihohi uku na kasar, ciki har da jihar Imo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Imo - Harbe-harben bindiga ya canja yanayin sanyin safiyar yau a makarantar Amaimo Central, gundumar Amaimo, karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo, yayin da mazauna yankin suka fito domin kada kuri'a a zaben gwamna da ke gudana.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kori masu zabe a Bayelsa, sun yi harbe-harbe

Hankalin jama'a ya tashi a wajen zaben, bayan da jami’an ‘yan sanda suka yi arangama da wakilan jam’iyyar.

Rundunar 'yan sanda
An ce rikici ya barke tsakanin wakilan jam’iyyar da ‘yan sanda a karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo Hoto: The Nigerian Police
Asali: Twitter

Abin da ya jawo arangamar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta ruwaito cewa, rikicin ya fara ne lokacin da wasu wakilan jam’iyya suka dage da cewa kada jami’an ‘yan sanda su raka jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) zuwa daya daga cikin rumfunan zabe da ke unguwar.

An ce jami’an ‘yan sandan sun dage akan sai sun raka jami’an INEC tare da kayyakin zabe zuwa rumfar zaben.

Lamarin dai ya haifar da kace-nace tsakanin jami’an ‘yan sanda da wakilan jam’iyyar, in da ta kai ga jami'an yan sandan sun yi harbe-harbe saman iska don sama wa kansu hanya.

An Yi Hasashen Makomar Gwamna Uzodinma

An yi hasashen cewa Gwamna Hope Uzodinma shi ne zai lashe zaben gwamnan jihar Imo da za a gudanar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya bayyana.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Bayelsa: Jam’iyyar LP ta gamu da gagarumin matsala

Chizorom Ofoegbu, wani mai fashin baki kan al'amuran siyasa da aka fi sani da 'Ijele Speaks', yayi wannan hasashen yayin da ya ke tsokaci kan zaben jihar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel