Matsala Ta Kunno, Mata Ta Auri Mijin da Ba Ya Haihuwa Cikin Rashin Sani, Zamansu Ya Yi Tsami

Matsala Ta Kunno, Mata Ta Auri Mijin da Ba Ya Haihuwa Cikin Rashin Sani, Zamansu Ya Yi Tsami

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta shiga tashin hankali yayin da ta ba da labarin mijinta da ta aura shekaru 6 da suka gabata
  • A cewarta, mijin nata bai haihuwa, kuma ya ki zuwa neman magani, inda yace ya dangana ga ubangiji
  • A wani rubutun da aka yada a Twitter, jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu kan irin wannan lamari mai daukar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Wata mata ‘yar Najeriya ta zo kafar sada zumunta don neman shawari kan kitimurmurar da ke faruwa a gidan aure.

Wara matar mai suna @ruleyourspace a shafin Twitter ta rubuta cewa, wannan labari ya faru da wata ‘yar uwarta ce, inda tace sun yi auren saurayi da budurwa ne shekaru 6 da suka gabata; amma babu haihuwa.

Kara karanta wannan

“Na sha kuka”: Yar Najeriya ta yada hirar da ta gani a wayar mijinta

A cewar matar, an sha yin gwaje-gwajen gano daga ina matsalar rashin haihuwar take, inda bincike ya gano mijin ne ke da karancin maniyyi.

Aure ya yi tsami tsakanin miji da mata
Mata ta kulu saboda mijinta bai haihuwa | Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na dangana ga Allah, inji mijin

Sai dai, bayan da aka gano tushen batu, mijin ya ki zuwa neman magani, inda yace yana jiran abin da Allah zai aiko masa.

Matar ta matsu, domin yanzu shekarunta 37 kuma ta matsu ta samu haihuwa kafin lokaci ya kure mata a nan gaba.

A cewarta, su din duka ma’aikata ne a wani coci, inda tace idan zai yiwu ta samu saki daga mijinta zai fi komai sauki a gareta.

Ta kuma bayyana cewa, a baya-bayan nan ta hadu da wani mazawari mai da daya, kuma za ta aure shi idan mijin nata ya sake ta.

Mata ta shiga rudani

Hakazalika, ta ce ta shiga rudani yanzu, don haka take neman shawari daga ‘yar uwar tata da ta yada batun a Twitter.

Kara karanta wannan

Zaben Bayelsa: Tashin hankali yayin da yan daba suka farmaki yan PDP, an kashe 1, wasu sun jikkata

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun kuma bayyana ra’ayoyinsu da ba da shawarin da suke ganin zai kawo maslaha.

Wasu sun ba ta shawarin ta ci gaba da zama da mijinta, haka Allah ya kaddara, amma wasu suka ce ya kamata a rabaauren don ta samawa kanta farin ciki.

Wasu kuwa cewa suka yi, za su iya daukar dan riko su maida shi nasu kowa ma ya huta daga kai ruwa rana.

Rashin haihuwa a nahiyar Afrika

Rashin haihuwa daga mace ko namiji ba karamin lamari bane a al’ummar nahiyar Afrika duba da al’ada da kuma tsarin zamantakewa.

Kowa ya sani, aure wani al’amari ne mai daukar hankali kuma mai bayyana cikar dan Adam, amma haihuwa ne gishirin rayuwar aure.

Akan samu irin wadannan matsaloli kuma akan kai ga mafita ko kuma rabuwar aure saboda rashin fahimtar juna.

Daga mata gori, Allah ya share mata hawaye

Kara karanta wannan

Hatsarin trela da adai-daita sahu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa, wata 'yar Najeriya mai suna Hellen Bello ta haifi' yan uku bayan shekaru da dama tana jira.

Da ta je shafinta na Facebook don murnar nasarar da ta samu, Hellen ta ce a karshe Allah ya albarkace ta da yara uku a lokaci guda bayan shekaru da yawa ana mata gori.

Sabuwar uwar ta wallafa hotunan lokacin da take da juna biyu da kuma lokacin da jariranta suka iso duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel