Karin Kudin Wuta: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Fara Zanga Zanga

Karin Kudin Wuta: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Fara Zanga Zanga

  • Gamayyar kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shirya zanga-zanga a fadin Najeriya kan karin kudin wutar lantarki
  • Sanarwar ta fito ne a wata takarda da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka aike wa gwamnatin tarayyar Najeriya
  • Har ila yau kungiyoyin sun bayyana irin matakan da za su dauka matuƙar wa'adin da suka bayar ya cika ba a dauki mataki ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gamayyar kungiyoyin kwadago karkashin NLC da TUC sun bukaci gwamnatin Najeriya ta janye karin kudin lantarki ko ta fiskanci zanga-zanga a fadin kasar.

NLC and TUC
Kungiyar kwadago za ta fara zanga-zanga kan karin kudin wuta. Hoto: Nigerian Lobour Congress (NLC)
Asali: Facebook

'Yan kwadago na shirin zanga-zanga

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a cikin wata wasika da suka aika ga hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya (NERC).

Kara karanta wannan

Cin zarafin Naira: Kungiyar NCSO ta nemi EFCC ta kama dan takarar gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyoyin sun aike da wasikar ga sakataren gwamnatin tarayya, ministan kwadago, ministan makamashi da kamfanoni masu raba wuta a Najeriya.

Menene dalilin shiryawa gwamnati zanga zanga?

Kungiyoyin sun bada wa'adi ga gwamantin zuwa 12 ga watan Mayu ko ta fuskanci zanga-zanga mai muni a dukkan fadin kasar.

Daga cikin dalilan da kungiyoyin suka bayar na janye karin kudin sun ce karin zai jefa 'yan Najeriya cikin kuncin rayuwa.

A cikin wasikar, sun yi nuni da cewa gwamnatin ba ta yi la'akari da halin da 'yan Najeriya ke ciki ba wurin karin kuɗin.

A kan haka ne suka ce ba za su zuba ido ba suna kallo ƴan Najeriya na shan wahala saboda karin kudin da ba a gina shi bisa doka ba.

Kungiyar kwadago ta jefi NERC da zargi

Kungiyoyin kwadagon sun zargi hukumar NERC kan zama ƴar amshin shatan kamfanonin raba wuta a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Harajin 0.5%: SERAP na shirin maka gwamnatin Bola Tinubu a kotu nan da kwana 2

A cikin wasikar, sun ce hukumar NERC ta hada kai da kamfanonin raba wuta domin su cimma burinsu na neman kudi da gumin talakawan Najeriya.

Me zai faru idan ba a janye karin ba?

A karshe dai ƙungiyoyin kwadago sun baiwa gwmantin tarayya wa'adi zuwa ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu domin janye karin kudin wutar, cewar jaridar Punch.

Abin da zai biyo baya idan ba a dauki matakin da ya kamata ba shi ne za suyi kawanya a dukkan ofisoshin hukumar NERC da kamfanonin raba wuta a fadin Najeriya.

Kungiyar kwadago ta dakatar da zanga-zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar NLC ta yi bayanin dalilin da yasa ta sanar da dakatar da zanga-zangar kwanaki biyu da ta fara a ranar Talata.

A cewar shugaban kungiyar kwadagon, an cimma makasudin gudanar da zanga-zangar ne a ranar farko, wanda shine dalilin dakatar da tattakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel