Dalilan Da Suka Sa Kotun Zaben Kano Ta Tsige Gwamna Abba Yusuf

Dalilan Da Suka Sa Kotun Zaben Kano Ta Tsige Gwamna Abba Yusuf

  • Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida Gida na NNPP
  • Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ta gano cewa kuri’u 165,663 da aka kadawa gwamnan ba masu inganci bane saboda ba a sa hannu da sutanfi a kansu ba
  • Kotun ta gano Abba Yusuf ba dan NNPP bane a lokacin zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba.

Haka kuma, kotun zaben ta ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Kujerar Gwamnan Kano, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaɓe

Dalilan da suka sa kotun zabe ta tsige Abba Yusuf
Dalilin Da Yasa Kotun Zaben Kano Ta Tsige Gwamna Abba Yusuf Hoto: Dr. Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A wannan rahoto, Legit Hausa ta tattaro wasu dalilai guda uku da ya sa kotun zaben ta tsige Abba Yusuf daga kan kujerar gwamnan Kano. Ga su a kasa:

1. Rashin kasancewarsa dan NNPP a lokacin zaben

Da take zartar da hukunci ta yanar gizo, shugabar kotun zaben, Mai shari'a Oluyemi Akinatan-Osadebey, ta bayyana cewa Abba Yusuf ba dan NNPP bane a lokacin da aka yi zaben gwamnan jihar Kano, rahoton Leadership.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Zartawar kuri'u

Yayin yanke hukuncin, mai shari'a Akintan-Osadebay ta bayyana cewa an samu zartawar kuri'u a lokacin zaben wanda ya bai wa Gwamna Yusuf fifiko a zaben.

Ta bayyana cewa tazarar kuri'u da ke tsakanin yan takarar NNPP da APC bai kai yawan kuri'un da aka soke ba.

3. Haramtattun kuri'u

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Fadi Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Bauchi

Kwamitin mutum uku na kotun ya kuma yanke cewa kuri'u 165,663 na gwamnan ba halastattu bane.

Kamar yadda hukuncin ya bayyana, ba a sanya hannu da sutanfi a kan takardun zabe 165,663 ba, don haka ba su da inganci. Saboda haka kotun ta rage kuri'u 165,663 daga jimilar kuri'un da Abba Yusuf ya samu.

Kotun zaben a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bai wa gwamnan sannan ta bayar da shi ga Gawuna na jam'iyyar APC.

Gawuna da APC sun kalubalanci sakamakon zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris inda Abba Yusuf ya yi nasara kafin hukuncin kotun.

Kotun zabe ta tsige Abba gida gida, ta bai Gawuna nasara

A baya mun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Abba Ƙabir Yusuf daga kujerar gwamna, ta ayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben 18 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Yusuf, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel