Najeriya da Kasashe 119 Sun Amince da Kudurin Falasdinawa, Sun Yi Kira da a Tsagaita Wuta

Najeriya da Kasashe 119 Sun Amince da Kudurin Falasdinawa, Sun Yi Kira da a Tsagaita Wuta

  • Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'u kan yadda za a kawo karshen tashin-tashina a tsakanin Hamas da sojin Isra'ila
  • Yakin Hamas da Isra'ila ya kai ga mutuwar Falasdinawa da yawa, hakan na ci gaba da daukar hankalin duniya
  • Najeriya na daga kasashen da suka bayyana goyon bayansu kan tsakaita wuta da Isra'ila ke yi kan mutanen Gaza

Najeriya da wasu kasashe 119 ne a ranar Juma'a suka kada kuri'ar amincewa da kudurin da ke kira da a samar da "zaman lafiya mai dorewa" tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas a Gaza.

Har ila yau, tanasun amince da ci gaba da shigar da kayayyakin agaji da rayuwar yau da kullum a yankin na Zirin Gaza mai fama da takurar Isra'ila, rahoton Al-Jazeera.

Kudirin da kasashen Larabawa suka shirya ya samu kuri'u 120 na goyon baya, 14 na adawa da kuma 45 suka ki bayyana matsayarsu.

Kara karanta wannan

Gaza: Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Zargi Isra'ila Da Keta Dokokin Jin Kai

An yi zabe a MDD kan Isra'ila
Zaben da aka yi a MDD a batun yakar Gaza da Isra'ila ke yi | Hoto: timesofisrael.com
Asali: UGC

Makasudin kudurin da aka amince dashi

Kudirin da a yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta amince dashi matsaya ta mafi yawan ra'ayi na kasashe mambobin majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

To sai dai kuma wannan shi ne martanin farko a hukumance da Majalisar Dinkin Duniya ta yi tun bayan da Hamas ta kai hari kan Isra'ila da kuma martanin taron dangin da Isra'ila din ta ke ci gaba da yi.

A baya, wasu kasashe sun mika kudurin Majalisar Dinkin Duniya ta fito tare da yin Allah-wadai da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Yadda aka kashe Falasdinawa

A halin da ake ciki, Isra'ila ta kashe adadi mai yawa na Falasdinawa da ke rayuwa a Zirin Gaza tun bayan fara daukar martani ga harin Hamas.

An bayyana yadda a baya sojin Isra'ila suka farmaki asibitin da ya kai ga mutuwar kananan yara da mata masu yawa.

Kara karanta wannan

Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya

Ba yanzu gaba da fadace-fadace suka fara ba a yankin, hakan ya faro ne tun shigar Isra'ila yankin Gabashi tun bayan yakin duniya na biyu.

Biden ya ba da agaji ga Gaza

A wani labarin, shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya ba da gudumawar Dala miliyan 100 don taimakawa Gaza.

Biden ya ba da taimakon ne bayan ya dira a yankin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da Kungiyar Hamas, cewar TheCable.

Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 18 ga watan Oktoba bayan rikicin da ya barke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel