DHQ: Luguden Wutan Jirgin Yakin Sojojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga Sama da 100

DHQ: Luguden Wutan Jirgin Yakin Sojojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga Sama da 100

  • Sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a wani ruwan bama-bamai da suka yi a iyakar jihohin arewa biyu
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya, sojoji sun aika gomman da yan bindiga lahira, sun damƙe wasu
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya jero wasu nasarorin da sojoji suka samu cikin mako ɗaya

FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun soji sun sheƙe 'yan ta'adda sama da 100 a wani luguden wuta ta sama a iyakar jihohin Zamfara da Neja.

Jami'in hulɗa da jama'a na hedkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ne ya faɗi haka ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sojoji sun samu babbar nasara a yaƙi da yan ta'adda.
DHQ: Luguden Wutan Jirgin Yakin Sojojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga Sama da 100 Hoto: NigerianArmy
Asali: UGC

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi kan ayyukan da rundunar soji ta yi a faɗin sassan ƙasar cikin makon da ya gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Sha Kaye a Kotun Ƙoli, Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala

Da yake nuna hotunan nasarorin da rundunar sojojin saman Najeriya suka samu, ya ce ruwan bama-baman ya kuma ragargaji mahara da dama a wasu sassan kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙarin nasarorin sojoji a mako ɗaya

Buba ya ƙara da cewa a wani samame da dakarun soji suka kai gidan kwamandan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Neja, sun kama mayaƙa da dama tare da kwato kayyaki.

Ya ce a wasu ayyukan da sojoji suka gudanar a makon da ya gabata a sassa daban-daban na ƙasar nan, sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 73 tare da kama wasu 182.

A cewarsa, sojojin sun kuma kama wasu mutane 14 da ake zargin barayin mai ne, tare da kubutar da mutane 68 da aka yi garkuwa da su a yankin Kudu-maso-Kudu.

Kakakin DHQ yace dakarun sun daƙile yunkurin satar man da aka kiyasta ya kai na kimanin Naira biliyan 1.212 a kasuwancin haram.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Cafke Masu Safarar Makamai Ga Yan Ta'adda Tare da Kwato Babura 19 a Kaduna

“Bugu da kari, sojojin sun kwato makamai iri-iri 119 da alburusai kala daban-daban 1,537," in ji shi.

Mutane 18 Sun Tsallake Rijiya da Baya

A wani rahoton na daban Fasinjoji akalla 18 sun tsallake rijiya da baya yayin da mummunan hatsarin mota ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan.

Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan motar Bas mai cin mutum 18 ta taso daga Maryland a Legas ta nufi birnin Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel