Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu

Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani uba a yankin Jharkhand, da ke kasar Indiya ya shirya wani kasaitaccen biki domin yi wa diyarsa maraba da dawowa gida bayan mutuwar aurenta
  • Tsarin rabuwar auren ya dauka hankali a soshiyal midiya, yana mai karin haske kan sarkakiyar da mata ke fuskanta a cikin al'umma
  • Sakshi Gupta, diyar Prem Gupta, ta auri wani injiniya a watan Afrilun 2022, kawai sai ta gano cewa mijin na da wata matar

Wani uba a jiha Jharkhand ta kasar Indiya ya kafa tarihi ta hanyar shirya bikin dawowar diyarsa gida bayan mutuwar aurenta mai cike da kalubalea.

Uba ya shirya biki bayan mutuwar auren diyarsa
Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta Hoto: WION
Asali: Twitter

Me yasa Sakshi ta baro aurenta?

Wannan taro da aka yi wa lakabi da bikin rabuwar aure, ya dauka hankali a soshiyal midiya saboda ci gaban da ya samu a cikin al'umma da galibi suke rungumar al'adun gargajiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

Sakshi Gupta, diyar Prem Gupta, ta auri wani injiniya a watan Afrilun 2022, kawai sai ta gano mijinta ya rigada ya yi aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da take fuskantar tarin kalubale a gidan aurenta, Sakshi ta ruga wajen mahaifinta domin neman agaji.

Baya ga goyon bayanta da ya yi a shawarar da ta yanke na kashe auren nata, mahaifin nata ya kuma shirya kasaitaccen bikin dawowarta gida.

Prem ya shirya taro inda masu kide-kide da wasanni suka taru suka yi shagali yayin da Sakshi ta baro gidan surukanta.

Bidiyon taron ya yadu

An cika da murna a wajen sha'anin wanda ya yi kama da taron bikin aure.

Taron ya kalubalanci irin kyamar da ke tattare da mutuwar aure a cikin al’umma da ke matsawa mata zama a gidan aure duk rintsi duk wuya.

Prem Gupta ne ya fara wallafa bidiyon shagalin a soshiyal midiya, kuma tuni ya yadu a dandalin.

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

Da yake bayyana ra’ayinsa a dandalin sada zumunta na Facebook, Prem ya jaddada muhimmancin mutunta yara mata musamman idan suka fuskanci kalubale na mutuwar aure.

Ya rubuta:

"Idan auren diyarka ya fuskanci gagarumin matsala, kuma idan ya zamana mijin da yan uwansa ne suke da laifi, ka dawo da diyarka gida cikin mutunci da girmamawa saboda yara mata suna da daraja sosai."

Uba ya ce zai tallafawa diyarsa

Prem ya kuma bayyana cewa ko kadan bai fusata da abun da faru da diyarsa ba domin dai ba a dole a zaman aure.

Ya kuma bayyana cewa a lokacin auren, ya bai wa surukansa sadaki mai tsoka na Rupi 17 wanda a yanzu suke shirin dawo masa da shi kamar yadda yake bisa al'ada.

Gupta ya kuma fada ma The Hindu cewa bai riga ya yanke hukunci kan sabuwar rayuwar da za su yi ba, amma ko shakka babu za su bai wa diyarsu gudunmawa a kan duk hukuncin da ta yanke.

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Martanin wata bazawara

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wata bazawara don jin kalubalen da ta fuskanta a lokacin da aurenta ya mutu musamman daga bangaren iyayenta.

Saudatu Balarabe ta ce:

“Gaskiya ba karamin kalubale na fuskanta ba a lokacin da aurenta ya mutu. Kuma kada kice ko laifina ne, kawai kaddara ce ta kawo karshen aurenmu don auren soyayya muka yi da mijina.
“Sai da na shafe tsawon watanni ko gaisuwata mahaifina baya amsawa, gara ita mahaifiyata ta fahimce ni. Ya kamata iyaye su gane cewa irin wannan dole da ake yi wa mata don ganin basu fito daga gidan aurensu ba koda su ke cutuwa ba daidai bane. Irin wannan ne idan ya yi kamata ki ji ance mace ta kashe kanta ko ta kashe mijinta.
“Yanzu kai ya waye ya kamata a daina duba me mutanen gari za su ce idan diyarka ta dawo gida. Kamata ya yi ka rungume ta hannu bibbiyu sannan ka duba hanyar inganta rayuwar da za ta yi a gaba. Ba karamin dadi na ji ba kan labarin wannan uba da ya tarbi diyarsa bayan mutuwar aurenta, ya kamata iyaye su yi koyi da shi.”

Kara karanta wannan

“Wannan Aure Akwai Matsala”: Rudani Yayin da Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

Kwalejin lafiya ta fadi dalilin korar daliba

A wani labarin, mun ji cewa an yi ta rade-radin cewa makarantar ta kori Rahama wacce ta yi fice a dandalin TikTok da Instagram saboda wallafar da take yi a soshiyal midiya.

Sai dai kuma, makarantar ta yi watsi da rade-radin, tana mai cewa an kori matashiyar ne saboda rashin bin ka'idoji da tsarin kwalejin, rahoton Daily Nigerian.

Asali: Legit.ng

Online view pixel