Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Rarara Raddi Ganin Ya Caccaki Shugaba Buhari

Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Rarara Raddi Ganin Ya Caccaki Shugaba Buhari

  • A yammacin Alhamis dinnan, Alhaji Dauda Adamu Rarara ya yi wa tsohon shugaban Najeriyan wankin babban bargo
  • Bashir Ahmaad wanda ya yi aiki na shekaru kusan takwas da Muhammadu Buhari, ya fito ya kare mai gidansa daga suka
  • Tsohon hadimin ya ba Mai girma Buhari kariya, ya nema masa uzuri a raddin da ya yi wa mawakin da aka fi sani da Rarara

Abuja - Malam Bashir Ahmaad ya dauki lokaci ya maida martani ga shahararren mawakin. Legit ta fahimci an wallafa raddin ne a jiya a shafin Facebook.

Tsohon mai taimakawa Muhammadu Buhari ya kalli faifen da ake yawo da shi, kuma ya yi wa Rarara raddi kan batutuwan da ya kawo daya bayan daya.

Matashin yake cewa duk wakokin da Rarara ya yi wa tsohon shugaban kasar, an biya shi hakkinsa saboda haka babu dalilin fitowa ya na yin gori a yau.

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

Rarara
Shugaba Buhari tare da Rarara da Ganduje Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Matashin ya ce wasu dalilai biyu ne su ka tunzura shi har ya nemi wanke uban gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya kuma ya sake fitowa a shafinsa ya na zargin marokin da sukar tsohon shugaban kasa saboda ya samu kamun kafa a gwamnati mai-ci.

Bashir ya ce su na yi wa Rarara fatan alheri a kan wannan hanya da ya dauka, dama ya koka a kan yadda aka hana shi damar zama da Bola Tinubu.

Ana neman a hallaka Rarara?

A bidiyon da aka fitar, Dauda Adamu ya ce an nemi ganin bayan rayuwarsa a mulkin Buhari, aka karbe masa ‘yan sanda bayan kai masa hari a bana.

Yayin da aka kona masa gida, ofis da motoci, sai shugaban ‘yan sanda ya karbe jami’ansa, a cewarsa hakan ba komai ba ne illa neman hallaka shi.

Kara karanta wannan

Mutane 2 kaɗai Su ka fi Ni Yi wa Tinubu Kokari,Na Cancanci Kujerun Ministoci – Rarara

Rarara ya zargi gwamnatin da ta shude da gazawa ta fuskar tsaro musamman saboda garkuwa da mutanen Arewa da ake yi da ta’adi a titin Abuja.

A nan ma Bashir Ahmaad ya tunawa mawakin halin da Boko Haram su ka jefa al’umma a baya.

Zagin Buhari domin kamun kafar Tinubu

"Idan har Rarara yana tunanin sai ya zagi Baba Buhari ne zai samu shiga a wurin Shugaba Tinubu da gwamnatin sa, to muna yi masa fatan alheri a kan hakan."

- Bashir Ahmaad

MARTANI GA MAWAKI DAUDA RARARA

"Na kalli wani bangare na videon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar a yau, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki.
Bayan kammala kallon video na yi yunkurin bawa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge - zargen da yayi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a halkance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu.

Kara karanta wannan

“Na Yi Nadamar Tallata Buhari”, Rarara Ya Fadi Gaskiyar Abin Da Ya Faru a Gwamnatin APC, Bidiyo

Na farko, cikin videon, Rarara yayi ikirarin cewa wai gudunmawar daya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?
A batun gagarumar gudumuwar da mawakin ya ce ya Buhari da Tinubu, Bashir Ahmad ya ce hankali ba zai dauki maganar da Rarara yake yi ba.
Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a bashi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemistry, balle technology a cikin wannan batu?
To gaskiya wanda maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a bashi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne, domin kuwa wadannan maganganun na sa sun saba da kowane irin hankali da tunani, idan dai ba akwai rashin lafiya ba, to lalle akwai tsantsar jahilci. Babu hikima a cikin maganganun nasa ko kadan."

Kara karanta wannan

Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu

- Bashir Ahmaad

"Buhari ya inganta tsaro a lokacinsa"

"A kuma maganar da Rararan yayi da cewa wai a cikin shekaru bakwai na Baba Buhari ba a iya bin hanyar Abuja zuwa Kaduna, a zahirin gaskiya ba zan ce ba a samu matsalolin tsaro a hanyar ba, sai dai zan dan yi masa tuni da ya tuna baya a lokacin da Baba Buharin ya karbi mulki, ba ma maganar kidnapping ake yi a hanyar ba, Saboda matsalar da Boko Haram ta jefa yankin Arewa daga Abuja zuwa Kaduna sai an ci karo da shingen jami’an tsaro sama da goma, ba ma maganar daga Kaduna zuwa Kano ba, balle uwa uba, daga Kano zuwa Maiduguri. Duk wanda yake da hankali zai godewa Allah akan wannan.
Game da wakokin da yayi wa Baba Buhari, tunda Rarara yake yi masa waka, bai taba yi masa waka kyauta ba tare da an biya shi hakkin sa ba.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari Ya Yi Ya Jawo darajar Naira ta ke Karyewa a Yau – Sanatan PDP

A karshen magana daya da Rarara ya manta bai fada ba ita ce bai fito ya bayyanawa jama’a cewa Baba Buhari bai taba taimakon sa a rayuwarsa ba."

- Bashir Ahmaad

Asali: Legit.ng

Online view pixel