"Ba Saboda TikTok Muka Kori Rahama Saidu Ba, Ta Fadi Jarrabawa Ne" – Kwalejin Lafiya Ta Kebbi

"Ba Saboda TikTok Muka Kori Rahama Saidu Ba, Ta Fadi Jarrabawa Ne" – Kwalejin Lafiya Ta Kebbi

  • Kwalejin Koyon Aikin Jinya Ta jihar Kebbi ta yi martani kan zargin da ake yi mata na korar dalibarta, Rahama Saidu saboda tana TikTok
  • Makarantar ta ce ta sallami Rahama ne saboda ta fadi jarrabawa sannan ta yi fashin zuwa makaranta na tsawon lokaci ba tare da kwakkwaran dalili ba
  • Jihar Kebbi - Kwalejin Koyon Aikin Jinya Ta jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi, ta karyata batun korar dalibarta, Rahama Sa'idu, saboda TikTok

An yi ta rade-radin cewa makarantar ta kori Rahama wacce ta yi fice a dandalin TikTok da Instagram saboda wallafar da take yi a soshiyal midiya.

Sai dai kuma, makarantar ta yi watsi da rade-radin, tana mai cewa an kori matashiyar ne saboda rashin bin ka'idoji da tsarin kwalejin, rahoton Daily Nigerian.

Kwalejin ta ce Rahama Saidu ta fadi jarrabawa ne
"Ba Saboda TikTok Muka Kori Rahama Saidu Ba, Ta Fadi Jarrabawa Ne" – Kwalejin Lafiya Ta Kebbi Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Gaskiyar dalilin korar Rahama daga makaranta

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Yankewa Shahararren Likita Da Ya Lalata Yar’uwar Matarsa Daurin Rai Da Rai

Kamar yadda makarantar ta bayyana, an sallami dalibar daga makaranta ne saboda ta fadi jarrabawa sannan ta ku yarda da mamaita aji da aka yi mata kamar yadda yake a tsarin makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da makarantar ta fitar ta ce:

"Bisa ga tsarin makarantar, duk dalibin da ya yi fashin zuwa makaranta ko asibiti na tsawon makonni 3 ba tare da wani kwakkwaran dalili ba zai maimaita zangon karatu kai tsaye.
"Rahama Saidu ta fadi jarrabawa watanni biyar da suka shude, ta daina zuwa makaranta ba tare da wani dalili ba. Sannan ta ki amincewa da maimaita zangon karatu, bata amsa ko daya daga cikin tambayoyin da ake mata ba na jin ta bakinta wanda hakan ne ya yi sanadiyar korarta

Ba mu san Rahama yar TikTok bace

Sai dai kuma, sanarwar ta bayyana cewa makarantar bata san cewa Rahama yar TikTok bace.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Jam'iyyun da Za Su Fafata a Zaben Jihar Kogi a Wata Mai Kamawa

Sanarwar ta kara da cewar:

"Saboda haka, dukkanin zarge-zargen da Rahama ta yi makarantar ba gaskiya bane, bai da tushe balle makama kawai zargi ne na kokarin batawa kwalehin suna wanda ya kamata jama'a su yi watsi da su."

Yadda aka ba matashi jabun kudi a banki

A wani labari na daban, mun ji cewa wani ɗan Najeriya ya fusata inda ya caccaki wani bankin kasuwanci bayan sun ba shi kuɗaɗen jabu.

A jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa an ba shi tsabar kuɗi Yuro 5,000 na jabu, kuma ya gano ne kawai lokacin da abokinsa ya je canja kuɗin zuwa fam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel