'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Benue Bayan Sace Shi Na Kwanaki

'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Benue Bayan Sace Shi Na Kwanaki

  • An bayyana yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka hallaka dattijon kasa bayan sace shi a watan Satumba
  • Tsagerun sun nemi kudin fansan da ya kai N12m a baya, daga baya suka nemi a ba su N5m don sake Erukaa
  • Ana yawan samun barnar 'yan bindiga masu sace mutane a jihohin Arewacin Najeriya a shekarun nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Benue - 'Yan bindiga sun kashe Washima Erukaa da suka yi garkuwa da shi a ranar 23 ga watan Satumba a gidansa da ke Zakibiam ta karamar hukumar Ukum a jihar Benue.

Washima wani dattijo ne da ya taba zama shugaban karamar hukumar Katsina Ala da Ukum a jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Basarke Da Mutum 5 a Zamfara

An kashe shugaban karamar hukuma a Benue
An kashe tsohon shugaban karamar hukuma a Benue | Hoto: Dan Mashin
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro daga wani amintaccen dan gidan mamacin cewa, masu garkuwa da mutanen sun sanar da su cewa Erukaa, mai shekaru 80 ya mutu a hannunsu kuma tuni suka binne shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bakin majiyar dangi

A cewar majiyar:

“Daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da shi ya sanar da wani dangin mamacin cewa Erukaa ya mutu tun tuni kuma sun binne shi don haka kada ma su yaudare mu da biyan kudin fansa.
“Da fari wadanda suka sace shi sun fara neman Naira miliyan 12 a matsayin kudin fansa amma daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 5.”

Har yanzu dai kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Kate Aneene, bai tabbatar da kisan dattijo Erukaa ba.

Ba wannan ne karon farko da ake sace mutane a jihar Benue ba, an sha yin hakan kuma an sha kashe wadanda aka sace a lokuta mabambanta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Mutane Sama da 20 Sun Jikkata Yayin da Wani Abu Ya Fashe a Jihar Kaduna

'Yan bindiga sun yi danyen aiki a Katsina

A wani labarin kuma, akalla mutum hudu ciki har da dan sanda guda daya ne aka kashe yayin da aka yi awon gaba da wasu da dama a lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari a Domawa a karamar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina a daren ranar Alhamis.

An kuma sace wasu 'yan mata biyar da wani mutum daya a wani hari na daban da aka kai Sukola, da ke karamar hukumar Bakori a jihar.

Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya na cewa 'yan ta'addan sun kai hari a cikin kauyen na Domawa ne 'yan mintuna kadan bayan karfe 9:00 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel