Gwagwalada Abuja
Barayi sun haura har gida tsakar rana sun sace ragon layya a birnin tarayya Abuja. Barayin sun shiga gidan ne tsakar rana yayin da mutumin ya fita.
Rundunar yan sanda a birnin tarayya Abuja ta yi nasara kan gungun barayi masu garkuwa da mutane tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a dazuka.
Yayin da ake cikin matsin halin tsadar rayuwa, darajar Naira ta sake faduwa a kasuwanni bayan samun habaka a kwanakin baya da kudin Najeriya ta yi.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya yi barazanar katse wutar ma'aikatun gwamnatin tarayya guda 24 da sauran abokan hulda kan rashin biyan kudin wutar.
Rikici ya kaure tsakanin wasu masu baban bola da mutanen unguwar Byazhin da ke kauyen Kubwa a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Hukuma mai kula da birnin tarayya Abuja ta ba shaguna 500 wa'adin sa'o'i 24 domin su tashi. Hukumar ta ce za ta rusa shagunan ne saboda an gina su ba bisa ka'ida ba.
Dalibar jami'ar Abuja da ta bata ranar Jumu'ah ta rasu a hatsarin mota a hanyar Ludbe. Iyalan dalibar ne suka fitar da sanarwa a jiya Litinin da yamma
Jami'an hukumar FCCPC sun gana da masu babban kantin 'yan kasar Sin wanda ake zargi da nuna wariya ga 'yan Najeriya. Sun yi musu tambayoyi masu yawa.
Wasu ɓarayin babura sun yi awon gaba da baburan jama'a yayin da ake tsaka da sallar tarawihi a kauyen Paso da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada a Abuja.
Gwagwalada Abuja
Samu kari