Kar Ku Bari ‘Yan Bindiga Su Karasa Mu – ‘Dan Majalisa Ya Kai Kuka Wajen Gwamnati

Kar Ku Bari ‘Yan Bindiga Su Karasa Mu – ‘Dan Majalisa Ya Kai Kuka Wajen Gwamnati

  • Yusuf Kure Baraje ya kai kuka game da yadda ‘yan bindiga su ka addabi mutanen yankinsa, su na yi masu dauki dai-daya
  • ‘Dan majalisar ya fadakar da gwamnatin tarayya cewa sojoji sun san inda miyagu su ka fake idan dai ana son ganin bayansu
  • Hon. Yusuf Baraje ya na magana ne a madadin mutanen Bosso/Paikoro a Jihar Neja da ya ke wakilta a majalisar wakilai

Abuja - Yusuf Kure Baraje mai wakiltar mazabun Bosso/Paikoro a majalisar wakilan tarayya ya yi kira ga gwamnati ta ceci mutanensa.

A ranar Talata, Leadership ta rahoto Hon. Yusuf Kure Baraje ya na rokon gwamnatin tarayya ta yi masu maganin ‘yan bindiga a yankinsu.

A hirar da aka yi da shi, ‘dan majalisar wakilan ya kuma nuna rashin tsaro ya yi tasiri a Bosso da Paikoro wajen rabon abinci da aka yi.

Kara karanta wannan

Tinubu da ECOWAS na Cikin Barazana, Majalisa Ta Ce a Gaggauta Wangale Iyakokin Arewa

Majalisa
'Yan Majalisar Wakilai Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Ganin al’umma ta shiga mawuyacin hali, gwamnatin tarayya da jihohi sun rabawa al’umma tallafi na rage radadin tsadar farashin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Kure Baraje ya fallasa jami'an tsaro

Yusuf Kure Baraje ya zargi da sojoji da rashin yin abin da ya dace domin kawo zaman lafiya, ya yi kira ga gwamnati ta ga bayan miyagun.

"Alal misali an kai hare-hare fiye da 10 a kauye na, ‘yan bindiga sun zo har zaure na domin kai mani hari.
Babu wanda ya iya zuwa nan, lokacin da jami’an tsaro su ka iya zuwa shi ne yayin sintirinsu daga Kantiri.
Amma yanzu maganar da na ke yi da ku, ban taba ganin dakarun sojoji da za su yaki ‘yan bindiga ba."

- Hon. Yusuf Kure Baraje

Ta'adin 'yan bindiga lokacin kaka

‘Dan majalisar yake cewa sojoji sun san inda ‘yan ta’addan su ke domin su na shigowa garuruwa irinsu Lambatta, su na sace Bayin Allah.

Kara karanta wannan

Ba Tinubu Ya Ci Zabe Ba – Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Fadi Asalin Wanda Ya Yi Galaba

Da zarar ruwa ya dauke a kogi, ‘dan majalisar ya ce mutanen yankinsa za su shiga uku domin ‘yan bindigan za su iya tsallake rafi cikin sauki.

Gwamna Zulum ya bada wa'adi

Mai girma Gwamnan Borno ya gano barnar da ake yi, sai ya dauki matakin gaggawa kamar yadda labari ya zo mana a farkon makon nan.

Babagana Umara Zulum ya bada umarni a ruguza masa gidajen da ake lalata da ‘yan mata da wani wurin da aka gano ‘yan kwaya na fakewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel