Shahararriyar Yar Kasuwa a Arewa, Laylah Othman Ta Auri Dan Majalisar Tarayya

Shahararriyar Yar Kasuwa a Arewa, Laylah Othman Ta Auri Dan Majalisar Tarayya

  • Fitacciyar yar kasuwar kuma mai kare hakkin mata, Laylah Ali Othman ta shiga daga ciki
  • An kulla aure tsakanin Laylah da angonta, Yusuf Gagdi a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba
  • Angon nata ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ta jihar Filato

Shahararriyar 'yar kasuwar nan ta arewa wacce ta yi fice a bangaren kayan alatu da kawata gida, Laylah Ali Othman ta shiga daga ciki.

An daura auren Laylah da angonta, Yusuf Gagdi, wanda ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ta jihar Filato a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Laylah ta auri dan majalisar tarayya
Shahararriyar Yar Kasuwa a Arewa, Laylah Othman Ta Auri Dan Majalisar Tarayya Hoto: Sheikh Abdoul Amrabat
Asali: Facebook

Matashiyar da kanta ce ta sanar da labarin auren nata a cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram.

Tana da kamfaninta mai suna L and N Interiors’, sa’annan tana sana’ar buga mujallun zamani, sannan ta kasance yar kare hakkin mata.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Damke Wani Mutum Kan Satar Buhun Shinkafa 47 Wanda Ya Kai Miliyan 2.5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga shahara da ta yi a bangaren kasuwanci, Laylah ta yi suna sosai a bangaren jin kai da tallafawa marasa gata.

A shekarun baya ne ta karbi rikon wani karamin yaro da aka tura almajiranci wanda ya hadu da ibtila'i har aka samu wasu suka ci zarafinsa. Ba shi kadai ba, matashiyar ta kuma karbi rikon wasu yara irinsa wadanda aka gani suna wangariri a titi.

Taimakon baya-bayan nan da ta yi shine na tallafawa wata baiwar Allah da ta karbi rikon wani maraya duk da kangin rayuwa da take ciki.

Laylah ta ginawa matar sabon gida kasancewar wanda take rayuwa a ciki bai da kyan gani kuma bai kamaci zaman dan adam ba, sannan kuma ta tallafa mata da jari.

Ga wallafar tata a kasa:

Jama'a sun taya Laylah murnar shiga daga ciki

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo Yayin da Majalisa Ta Samo Mafita Kan Farashin Kaya, Ta Tura Sako Ga Tinubu

Legit Hausa ta tattaro martani wasu mabiyan matashiyar wadanda suka taya ta murnar cike rabin addininta.

meemaestee1 ta yi martani:

"Masha Allah Masoyiyata…..❤️ Allah ubangiji ya baku zaman Lafiya, Allah ya kauda idon makiya, ya kauda masu kambun baka. Laila a wannan rana, Ina miki fatan alkhairi a wannan sabon feji na rayuwarki. Na fi kowa murna, ina kaunarki a kodayaushe❤️"

realalinuhu ya yi martani:

"Allahu Akbar, Allah ya bada zaman lafiya."

alhanislam ta ce:

"Allah bada zaman lafeeya❤️"

meenaceleb ta yi martani:

"Masha Allah, Alhamdulillah, tabarakallah. Am so so happy for u dear. Allah ya baku zaman lafiya."

surykmata ta ce:

"Allah ya sanya muku dukkan alkhairanSa da albarka ameen. Fi Amanallah ❤️❤️❤️"

Legit Hausa ta tuntubi Hajiya Laylah ta shafinta na Instagram don jin karin bayani daga wajenta dangane da wannan aure nata da kuma kan wasu ayyukan taimako da take yi wa al’umma ta gidauniyarta, amma bata amsa ba zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudi: Yadda Shagalin Bikin Wadda Ta Auri Kanta Da Kanta Ya Gudana

Yadda aka sha shagalin bikin wata da ta auri kanta

A wani labarin, mun ji cewa wata mata da ta shafe tsawon shekaru 20 tana tara kudi don yin kasaitaccen biki da take mafarki ta auri kanta da kanta bayan ta gaza samun abokin rayuwa da ya dace da ita.

Sarah Wilkinson, mai shekaru 42 a duniya ta yanke shawarar yin shagalin biki wanda shahararriyar aminiyarta ta gudanar a Harvest House da ke Felixstowe, Suffolk, rahoton BBC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel