Majalisar Wakilai Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Hukumar Kula da Farashin Kaya a Najeriya

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Hukumar Kula da Farashin Kaya a Najeriya

  • Yayin da ake cikin matsin tashin farashin kayayyaki a Najeriya, Majalisar Wakilai ta fara nemo hanyar kawo sauki
  • Majlisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa wata hukuma da za ta kula da kuma kayyade farashin kayayyaki a kasar
  • Mamban majalisar, Hussaini Mohammed Jalo shi ya nemi wannan bukatar ga majalisar yayin zamanta a jiya Alhamis

FCT, Abuja – Majalisar Wakilai a Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kafa hukuma da za ta kayyade farashin kaya a kasar.

Wannan ya biyo bayan wani kudiri da mamban majalisar Hussaini Mohammed Jalo ya yi a jiya Alhamis 12 ga watan Oktoba.

Majalisa ta bukaci Tinubu ya kafa kwamitin kayyade farashin kaya
Majalisar Wakilai ta fara nemo hanyar rage farashin kaya a kasar. Hoto: National Assembly.
Asali: Facebook

Meye majalisar ke cewa ga Tinubu kan farashin kaya?

Yayin gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce ya kamata a dauki mataki kan tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Ban Gaji Ko Kwandala a Baitul-Mali Ba" Gwamnan APC Na Arewa Ya Fallasa Yadda Ya Karɓi Mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan ya biyo bayan tsadar man fetur dalilin cire tallafi da kuma tashin Dala a kasuwanni.

Har ila yau, ya ce ya kamata majalisar ta bukaci ma’aikatar kasuwanci don ganin an samar da hukuma da za ta rinka kula da farshin kayayyaki a Najeriya.

An karbi kudirin da kuma mika shi ga kwamitin majalisar da ke kula da bangaren kasuwanci don daukar matakin gaba.

Legit Hausa ta ji bakin wasu kan wannan lamari

Musa Hussaini ya ce wannan mataki gaskiya zai taimaka daman tuntuni abin da su ke nema kenan.

Aisha Hussaini ta ce:

"Idan har hakan zai samu, abin farin ciki ne daman jama'a na cikin kunci."

Kabiru Umar ya soki Tinubu inda ya ce babu wani kafa hukuma da zai yi kan matsalar.

Ya ce da ya shirya hakan da ya sanar tun sanar da ya sanar da cire tallafi a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Wuff da Fitacciyar Yar Kasuwar Nan a Arewa Laylah Othman

Meye ya jawo tashin farashin kayan a kasar?

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke fama da tashin farashin kaya tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu.

Shugaba Tinubu bayan cire tallafin ya yi wa ‘yan kasar alkawarin samar musu da wani tallafi da zai rage radadin cire tallafin da aka yi.

Daga bisani shugaban ya ware Naira biliyan biyar ga ko wace jiha da ke kasar 36 da kuma birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Sai dai tallafin ya bar baya da kura yayin da ake zargin gwamnonin jihohi da karkatar da tallafin ta wata hanya, cewar Ripples.

Tinubu ya ware Naira biliyan 5 ga jihohi don rage radadi

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya ware Naira biliyan biyar ga jihohin Najeriya 36 da birnin Tarayya Abuja don rage radadin cire tallafi.

Tinubu ya ware kudaden ne kamar yadda ya yi alkawari bayan cire talafin a watan Mayu na wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.