"Ba Gaggawa Na Ke Yi Ba", Janar Yakubu Gowon Ya Magantu Kan Jita-Jitar Mutuwarsa

"Ba Gaggawa Na Ke Yi Ba", Janar Yakubu Gowon Ya Magantu Kan Jita-Jitar Mutuwarsa

  • Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya ya yi magana kan rahotannin cewa ya riga mu gidan gaskiya
  • Tsohon shugaban na Najeriya ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labarai ya ce lafiyarsa kalau kuma yana nan da ransa kana ba gaggawa barin duniya ya ke yi ba
  • Gowon ya mulki Najeriya ne daga watan Agusta na shekarar 1966 zuwa 29 ga Yulin shekarar 1975 kuma a zamaninsa kasar ta tsinduma yakin basasa da masu neman kafa Biyafara

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya karyata rahoton cewa ya mutu kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka wallafa.

A cikin wani sako da NTA ta fitar a kafar X, hadimin tsohon shugaban mulkin sojan ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya ce lafiyarsa kalau kuma yana nan da ransa, ya kara da cewa ba gaggawar mutuwa ya ke ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Nada Shugaban ICPC, Ana Duba Yiwuwar Dauko Bakano ‘Dan Shekara 71

Yakubu Gowon ya karyata jita-jitar cewa ya mutu
Yakubu Gowon ya ce ba gaggawa ya ke ya mutu ba.
Asali: Twitter

Ga sakon a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina nan har yanzu kuma lafiya ta kalau. Ba gaggawa na ke ba"

Gowon shine shugaban mulkin soja na uku a Najeriya bayan kasar ta samu yancin kai a shekarar 1960.

A lokacin mulkinsa ne kasar ta tsinduma cikin yakin basasa, wacce aka shafe watanni 30 ana tafkawa.

Tsohon shugaban na mulkin soja wanda ya jagoranci kasar tsakanin 1 ga watan Agustan 1966 zuwa 29 ga Yulin, 1975, yana cikin wadanda suka kafa kwamitin zaman lafiya ta kasa a 2005.

Dan Majalisar Kasar Birtaniya Ya Zargi Yakubu Gowon Da Sace Rabin Kudin CBN

A wani rahoto daban wani dan majalisar kasar Birtaniya ya fito ya yi ikirarin cewa Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya ya sace kudin mutanen kasa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

Dan majalisar wanda ya yi wannan jawabi na zargi a wani zaure ya yi ikirarin cewa Janar Gowon mai murabus ya yi awon gaba da rabin kudin da ke asusun babban bankin kasa CBN.

Amma wani binciken neman gano gaskiya da aka gudanar ya nuna cewa babu kanshin gaskiya cikin wannan zargi da mutumin ya yi.

Dan majalisar da aka rahoto sunansa a matsayin Tom Tugendhat ya yi wannan zargi ne a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba lokacin da yan majalisar na Birtaniya ke tattaunawa kan batun hukunta jami'an Najeriya da ake zargi sun keta hakkin bil-adama yayin zanga-zangar Endsars a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel